Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas Ya Tsallake Harin Kisan da Aka Kai Masa

Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas Ya Tsallake Harin Kisan da Aka Kai Masa

  • 'Yan bindiga sun farmaki tawagar ɗan takarar gwamnan SDP a jihar Ribas, Magnus Ngei Abe, ranar Litinin
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun bude wa tawagar kamfen ɗan takarar wuta a Akinima, kamar hukumar Ahoada ta yamma
  • Sanata Abe ya bayyana cewa wasu mutane ne suka ɗauki nauyin harin amma bai ambaci sunayensu ba

Rivers - Ɗan takarar gwamnan jihar Ribas a inuwar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP), Sanata Magnus Ngei Abe, ya tsallake mummunan harin kisan da aka kai masa ranar Litinin.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba suka kai mummunan harin kan tawagar yakin neman zaɓensa a kauyen Akinima, ƙaramar hukumar Ahoada-West.

Sanata Magnus Abe.
Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas Ya Tsallake Harin Kisan da Aka Kai Masa Hoto: leadership
Asali: UGC

Tun da fari, Sanata Abe da tawagarsa sun ziyarci ƙauyen Ubeta da wasu ƙauyuka a yankin daga bisani suka nufi Akinima, hedkwatar karamar hukumar, lokacin da aka kai masu kazamin hari.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ainihin mutanen da ke boye sabbin kudi, suna siyarwa a boye a Arewa

A wani gajeren bidiyo dake yawo a soshiyal midiya an hangi mambobin tawagar kamfen ɗan takarar suna turereniyar gudun neman tsira yayin harin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake jawabi kan abinda ya faru, Sanata Abe ya ce:

"Muna hanyar zuwa ashe sun rigamu sun gitta Motoci biyu domin toshe mana hanya saboda kar mu wuce. Mulkin Demokaradiyya ake a Najeriya kowa yana da 'yancin zuwa ya gana da mutane."
"Idan ka shugabanci mutane na tsawon shekara Bakwai ya kamata mutane su rika farin ciki a kanka, idan basu jin daɗinka to hakan ta faru ne saboda baka tsinana masu komai ba."
"A yanzu ka koma kana turo 'ya'yan wasu su zo su toshe 'yan siyasa daga tattaunawa da al'umma."

Jaridar Tribune ta tattaro cewa ɗan takarar gwamna a inuwar SDP bai bayyana suna ƙarara na waɗanda yake nufi da kalamansa ba.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: CBN Ta Fara Sabon Tsarin da Mutane Zasu Ji Dadi Wajen Samun Sabbin Kuɗi

Gwamnan Wike Ya Kara Daukar Zafi Kan Ayu

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya zargi shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa da yunkurin cin amanar jam'iyya

Wike , jagoran tafiyar tawagar gwamnonin G-5 yace ba zasu zuba ido suna kallo ba domin irin wannan matakin na bukatar martani mai zafi daga PDP reshen Ribas.

A cewasa babu wanda zai taɓa jihar Ribas ya kwana lafiya don haka wannan batu ba zasu barshi haka nan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel