Gwamna Wike Ya Tona Asirin Kwamitin Ayu Na Cin Amanar Jam'iyyar PDP

Gwamna Wike Ya Tona Asirin Kwamitin Ayu Na Cin Amanar Jam'iyyar PDP

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya zargi shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa da yunkurin cin amanar jam'iyya
  • Wike, jagoran gwamnonin G-5 yace Ayu ya umarci lauyoyin dake kula da kararrakin PDP a Ribas su tsame hannunsu
  • Gwamnan wanda ba ya shiri da shugabancin PDP ya yi ikirarin maida zazzafan martani kan wannan umarnin

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi zargin cewa shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya umarci lauyoyin dake kula da ƙararrakin jam'iyya a Ribas su janye.

Gwamnan ya bayyana wannan umarni da Ayu ya baiwa lauyoyin da manakisar cin amanar jam'iyya, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Gwamna Wike Ya Tona Asirin Kwamitin Ayu Na Cin Amanar Jam'iyyar PDP Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike, jagoran tafiyar tawagar gwamnonin G-5 yace ba zasu zuba ido suna kallo ba domin irin wannan matakin na bukatar martani mai zafi daga PDP reshen Ribas.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyun Siyasa 40 Sun Yanke Shawara, Sun Fadi Wanda Zasu Marawa Baya Tsakanin Atiku da Tinubu

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa PDP reshen jihar ta kai ƙarar wasu jam'iyyu Kotu kan tuhumar ƙin biyayya da take dokokin hukumar zabe INEC yayin gudanar da zabukan fidda gwani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Wike ya yi wannan furuci ne a harabar makarantar jiha da ke Okehi 1, yayin kaddamar da kamfen PDP a ƙaramar hukumar Etche ranar Litinin.

Ya ce maimakon shugabancin jam'iyya na ƙasa ya goyi bayan ƙarar da PDP ta jiha ta shigar, sai kawai aka ji ta umarci lauyoyin da ke kula da ƙararrakin sun janye daga wakilcin shari'a.

A rahoton Channels tv, Wike ya ce:

"Mun gano su, su ne suka koma cin amanar jam'iyya, na faɗa masu zagon ƙasa da cin amana ne ya haifi cin amana. Kunsan mun kai ƙarar waɗan nan kananan jam'iyyun Kotu saboda gaza bin tanadin doka."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Daba Sun Kai Hari Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamnan PDP

"Mutanen Abuja da suke alfaharin suna matakin ƙasa sun ɓushe da haɗa kai da su (jam'iyyun siyasa) sun rubuta wasika ga lauyoyi da umarnin su tsame hannu domin kashe Kes din da muka kai."
"Na faɗa wa Lauyoyin mu su janye daga batun, zan maida masu martani zuwa gobe. Ba wanda zai taɓa mu ya kare lafiya, duk wanda ya yi gigin taɓa mu a Ribas zamu barshi da tabo kuma mun fara."

APC ta kara rasa yan majalisu uku a Katsina

A wani labarin kuma Yan Majalisar Wakilan Tarayya Uku Sun Fice Daga APC, Sun Koma PDP

Mambobin majalisar wakilan tarayya uku daga jihar Katsina sun tattara kayansu daga APC sun koma jam'iyyar PDP.

Rahotanni sun bayyana cewa yan majalisun sun yanke shawarin shiga PDP ne bayan ganawa da Atiku Abubakar a jihar Sakkwato ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel