Tsohon Shugaban Jami'ar Bayero Ta Kano, Farfesa Umar, Ya Rasu

Tsohon Shugaban Jami'ar Bayero Ta Kano, Farfesa Umar, Ya Rasu

  • Allah ya yi wa tsohon shugaban Jami'ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Ibrahim Umar rasuwa
  • Marigayin wanda ya rasu a ranar Litinin shine mutum na uku da ya jagoranci jami'ar ta BUK tun kafuwarta
  • Shugaban BUK na yanzu Farfesa Sagir Abbas ya yi bakin rasuwar Farfesa Umar ya kuma mika ta'aziyya ga daukakin jami'ar ta iyalansa

Jihar Kano - Fitaccen likita kuma tsohon shugaban jami'ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Ibrahim Umar ya riga mu gidan gaskiya.

Dansa, Farouk Ibrahim Umar ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa, a ranar Litinin yana mai cewa za a yi jana'izarsa a Kofar Kudu misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata, Daily Trust ta rahoto.

Farfesa Umar
Tsohon Shugaban Jami'ar Bayero Ta Kano, Farfesa Umar, Ya Rasu. Hoto: Farfesa Umar
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Zargin Jifan Buhari a Kano: APC Ta Yi Martani Mai Daukar Hankali, Ta Fadi Gaskiya

Marigayin, wanda ya jagoranci BUK tsakanin 1979 da 1986, shine shugaban jami'ar na uku.

Shine dan Najeriya na farko da ya fara koyar da Physics a jami'ar a shekarar 1976.

A hirarsa na karshe da Daily Trust a 2017, marigayin ya yi waiwaye inda ya bayyana mukamai daban-daban da ya rike a kasa da waje, ciki har da wakiltar Najeriya Kwamitin Makamashi na Duniya daga 1990 kuma yana cikin tawagar da ta tsara kundin tsarin mulkin kasa na 1979.

Yana cikin tawagar Najeriya da ta tafi taron Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya na Kasa da Kasa, IAEA, daga 1989 kuma aka nada shi shugaba Hukumar Makamashi na Najeriya a 1989.

Ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin IAEA daga 2000-2001 kuma a 2004 shine direkta na cibiyar binciken makamashi da horaswa, inda na'urar bincike na nukiliya na farko a kasar ya ke.

Mukamin da aka sani ya rike na karshe shine a 2007, lokacin da aka nada shi a kwamitin bada shawarwari na kasa da kasa kan makamashi wanda ake sabunta shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar PDP Ta yi Alla-Wadai Da Rajamun Da Aka Yiwa Shugaba Buhari a Kano

A hirar, ya shawarci yan Najeriya 'su tabbatar sun zabi mutane wadanda za su yi wa kasa aiki ba don za su bawa mutane kudi ba' a matsayin daya cikin hanyar warware kallubalen da ke damun kasar.

Martanin shugaban BUK na yanzu kan rasuwar Farfesa Umar

Shugaban Jami'ar BUK na yanzu, Farfesa Sagir Abbas, ya bayyana bakin ciki kuma ya yi ta'aziyya ga daukakin jami'ar.

Ya ce marigayin ya aza tushe mai kyau a lokacin da ya ke shugabancin jami'ar kuma taka muhimmin rawa wajen fadada jami'ar musamman new site.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel