Ina Jin Tsoro: Matashi Ya Shiga Tashin Hankali Yayin da Za a Tsira Masa Allura a Asibiti, Bidiyon Ya Yadu

Ina Jin Tsoro: Matashi Ya Shiga Tashin Hankali Yayin da Za a Tsira Masa Allura a Asibiti, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani gansamemen saurayi ya je asibiti don yin gwaji amma ya razana sosai da aka zo batun dibar jininsa don gwaji
  • Mutumin ya rasa sukunin bari ma'aikaciyar jinyan ta soka masa allura a hannu don daukar jinin nasa
  • Yana ta ihu ita kuma ma'aikaciyar asibitin ta dungi zare alluran har sai da wani ya rike shi

Masu amfani da TikTok 556 sun yi martani a kan bidiyon wani gansamemen mutum wanda ke tsoron allura.

Mutumin ya je asibiti inda wata malamar jinya ta yi kokarin soka allura a daya daga cikin yatsunsa don karbar jinin da za a yi gwaji.

Matasa
Ina Jin Tsoro: Matashi Ya Shiga Tashin Hankali Yayin da Za a Tsira Masa Allura a Asibiti, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@carthyrinah.
Asali: UGC

Maimakon ya nutsu sannan ya bari a diba jinin, sai ya dunga kaduwa cike da tsoro sannan ya zura idanunsa kan alluran.

Bidiyon wani mutum da ke tsoron allura a asibiti

Kara karanta wannan

Bidiyo: Leburori Sun yi Sama da Abokin Aikinsu, Duk a Cikin Murnar Cin Jarabawa da Yayi

Kaduwar da mutumin ya dungi yi ya hana malamar jinyar yin aikinta yadda ya kamata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani mutumi da ya rako matsoracin mutumin ya taimaka masa amma yana ta ture hannunsa.

Ihu da rawan da jikinsa ya dungi yi ya haddasa dirama a asibitin. Sai da aka dauki tsawon lokaci kafin ma'aikaciyar jinyar tayi nasarar diban jinin.

Bidiyon wanda @carthyrinah ta wallafa ya yadu kuma ya ba da dariya a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@CarolineN ta ce:

"Majinginar wata kenan."

@merctmelc2 ta ce:

"Zan iya mutuwa a kan ki. Ba zai iya jure allura a kansa ba."

@stacydesa ta yi martani:

"Kuma yana kiran kansa namiji."

Matashi ya yi barazanar tarwatsa banki yayin da mai gadi ya hana shi shiga ciki

A wani labari na daban, wani dan Najeriya ya dauki zafi sosai bayan ya isa banki don shigar da tsoffin kudadensa tare da samun sabbi.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Matashi Dan Najeriya Ya Dau Zafi, Ya Yi Barazanar Tarwatsa Banki Yayin da Jami’an Tsaro Suka Hana Shi Shiga a Bidiyo

Mutumin dai ya isa banki da jakar kusinsa inda ya tarar da cunkoson jama'a da ke kokarin shigar da nasu kudaden.

Sai dai kuma, mai gadin bankin ya kekyashe kasa ya hana masa shiga ciki inda shi kuma hakan ya tunzura shi har yana barazanar tayar da zaune tsaye.

Mutane da dama da suka ci karo da bidiyon sun sha dariya a manhajar TikTok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel