EFCC Ta Kame Wasu Mutane a Abuja da Siyar da Sabbin Naira Ga Mutane

EFCC Ta Kame Wasu Mutane a Abuja da Siyar da Sabbin Naira Ga Mutane

  • Hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC ta kame wasu da ake zargin suna dillacin Naira da Naira a Najeriya
  • An kama mutanen ne daidai lokacin da ake ci gaba da koka karancin kudi tare da jin ana siyar da kudi a wasu jihohin kasar
  • Babban bankin Najeriya ya kara wa'adin daina amfani da tsoffin kudade a kasar zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu

Abuja - Hukumar EFCC a babban birnin tarayya Abuja ta yi nasarar kame wasu da ake zargin suna boyewa tare da siyar da sabbin Naira da aka buga a kasar nan, Channels Tv ta ruwaito.

Kakakin EFCC, Wilson Uwajaren ne ya bayyana hakan a Abuja, inda yace an kama mutanen ne a yankin Zone 4 da kuma Dei Dei a ranakun Asabar da Litinin.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ɗan Takarar Gwamna a 2023 Kazamin Hari, Sun Bude Masa Wuta

Ya bayyana cewa, kamun ya yiwu ne bayan samun bayanan sirri da ke zargin wasu bata-gari da boye sabbin Naira tare da siyar dasu ga mutane kan farashi mai tsada.

An kama masu siyar da sabbin Naira a Abuja
EFCC Ta Kame Wasu Mutane a Abuja da Siyar da Sabbin Naira Ga Mutane | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana cewaa, wadanda aka kamen sun yi bayanai masu daukar hankali, ciki har da bayyana wadanda ke basu sabbin kudade a bankuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta kuma yi alwashin cewa, za ta ci gaba da fakewa a bakin bankunan kasar nan sai ta kame dukkan masu sana'ar siyar da kudi.

Ku nesanci irin wannan halin, EFCC ga 'yan Najeriya

Daga nan ta gargadi 'yan Najeriya da su nesanta kansu da irin wannan mummunan aikin, kana suna ce hakan zai kai ga kamu da kuma hukuncin doka mai tsanani.

A tun farko, gwamnN CBN ya fito ya yi bayani, ya ce bankin zai hada kai da EFCC da ICPC domin tabbatar da kame masu bata sunan Najeriya ta hanyar boye sabbin kudi, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: 'Yan bindiga sun daina karbar kudin fansa, sun tsiro da wata hanyar

Idan baku manta ba, a yanzu haka a Najeriya an yi sabbin N200, N500 da N1000, kuma za su daina amfani daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Mutanen kauye sun godewa CBN bisa tura wakilai

A wani labarin kuma, kunji yadda mazauna kauyuka ke yiwa CBN godiya bisa kai musu wakilai da ke ba musayar kudi

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da CBN yace zai tura wakilansa don saukaka hada-hadar kudi a jihohi.

Mutanen kauyuka a Najeriya sun bayyana bacin rai da tsoron halin da za su shiga game da sauyin kudi a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel