Jam’iyyar PDP Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kaiwa Shugaba Buhari a Kano

Jam’iyyar PDP Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kaiwa Shugaba Buhari a Kano

  • Jam'iyyar PDP ta yi watsi da farmakin da wasu fusatattun mutane suka kaiwa Shugaba Buhari a jihar Kano
  • A yau Litinin, 30 ga watan Janairu, shugaban Najeriya ya kai ziyarar aiki jihar Kano, sai dai rikici ya barke bayan kaddamar da ayyukansa
  • Jam'iyyar adawar ta daura alhakin kai harin kan dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu da Gwamna Abdullahi Ganduje

Kano - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi Allah wadai da harin da wasu miyagu suka kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin zaiyarar da ya kai jihar Kano a ranar Litinin, 30 ga watan Janairu.

Yayin da take watsi da lamarin, jam'iyyar adawar ta bayyana shi a matsayin shiryayyen hari kan shugaban kasa wanda ta ce cin amanar kasa ce da tozarta ta wanda ya zama dole kowa ya yi Allah wadai da shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar PDP Ta yi Alla-Wadai Da Rajamun Da Aka Yiwa Shugaba Buhari a Kano

Buhari
Jam’iyyar PDP Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kaiwa Shugaba Buhari a Kano Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Tinubu da Ganduje ne suka shirya harin da aka kaiwa Buhar, PDP

PDP ta kuma zargi dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da daukar nauyin wannan farmaki da aka kaiwa shugaban kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren labaran jam'iyyar PDP na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ya fitar a yau Litinin.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Jam'iyyarmu ta kadu da cewar wannan hari na daga cikin makircin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC na yi wa fadar shugaban kasa zagon kasa, haddasa rudani, tayar da rikici a kasar, kawo cikas ga babban zaben 2023 da kuma kawo tangarda ga damokradiyyarmu, duba da ganin cewa ba zai iya lashe zabe ba cikin tsarin zabe na gaskiya da lumana.

Kara karanta wannan

'Barin Zance: Gwamnonin APC 3 Sun Jagoranci Tinubu Domin Kai Wa Buhari Ziyarar Dannar Ƙirji

"PDP ta ja hankalin yan Najeriya da su lura da yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi kokarin kawo tsaiko ga tafiyar shugaba Buhari sannan har ya yi kokarin hana shi kai ziyara jihar Kano.
"Abun da ya fi tayar da hankali shine yadda yakin neman zaben shugaban kasa na APC ya shirya tozarta shugaba Buhari tare da illata shi yayin da yake gudanar da aikinsa a Kano.
"A lura cewa dan takarar shugaban kasa na APC na ta nuna kyamar Shugaba Buhari a fili tare da yin kalamai marasa dadi a kansa tun bayan jawabin shugaban kasar, wanda ya yi daidai da tsarin damokradiyya da ake amfani da shi a fadin duniya, cewa a bari yan Najeriya su zabi duk dan takara da jam'iyyar da suke so a babban zaben 2023."

Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa a kwanan nan ne Asiwaju Tinubu ya kara tunzura magoya bayansa kan shugaba Buhari a wajen gangamin yakin neman zabensa a Abeokuta, jihar Ogun, inda ya zargi shugaban kasar da yunkurin yin murdiya a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe, Tinubu Ya Daukarwa Iyaye Gagarumin Alkawari Da Zai Cika Masu a Kan 'Ya'yansu

Ga cikakkiyar sanarwar a kasa:

An yi wa Buhari ihun ba ma yi bayan kaddamar da aiki a Kano

A baya mun ji cewa fusatattun mazauna jihar Kano sun gwabza da jami'an tsaro bayan ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai jihar inda ya kaddamar da ayyuka a ranar Litinin.

Matasan dai sun ta jifa da duwatsu domin nuna adawarsu da ziyarar da shugaban kasar ya kai jihar yayin da kasar ke cikin mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel