Latest
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da shirin rabon dabbobi ga mata domin dogaro da kansu. Ya gargadi wadanda za su ci gajiyar shirin.
Malam Dikko Umaru Radɗa ya kara kassara jam'iyyun adawa a Katsina, ya karbi dubban masu sauya sheka zuwa APC, ya ba da umarnin jawo su cikin harkokin gwamnati.
Tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya shiga matsala da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya kai kararsa kotu kan zargin bata masa suna da kiransa 'dan ta'adda.
Wata babbar kotun jihar Kaduna ta ki karbar bukatar samun beli ta tsohon kwamishinan kudi a gwamnatin Nasir Ahmad El-Rufai, Alhaji Bashir Sa'idu.
Wasu daga cikin gidajen mai a kasar nan sun fara gyara farashin litar fetur bayan matatar Dangote ta sanar da karin farashi, sannan an samu kari a duniya.
Wata tanka ta sake faɗuwa tana zubar da man gyaɗa, mutane sun sake tururuwa ɗibar ganima ba tare da fargabar abin da ya faru kwanakin baya ba a jihar Niger.
Kungiyar masu amfani da layukan sadarwa (NATCOMS) ta kalubalanci Hukumar NCC inda ta yi watsi da karin kudin tarho da cewa bai dace ba kuma zai kara wahala.
Hanu Fejiro Agbodje ya ce Najeriya na bukatar mallakar Bitcoin don bunkasa tattalin arziki, yayin da ake hasashen darajar Bitcoin za ta iya kai dala $180,000 a 2025.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yabi manufofin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Ya bayyana cewa za a ga amfaninsu nan ba da dadewa ba.
Masu zafi
Samu kari