Kotu Ta Jikawa Tsohon Jami'in Gwamnatin El Rufai Aiki, Ta Ki Karbar Bukatarsa

Kotu Ta Jikawa Tsohon Jami'in Gwamnatin El Rufai Aiki, Ta Ki Karbar Bukatarsa

  • Kotu ta ƙi amincewa da buƙatar neman beli da tsohon kwamishinan kuɗi a jihar Kaduna, Alhaji Bashir Sa'idu, ya nema a gabanta
  • Babbar kotun wacce ke jihar Ƙaduna ta ƙi karɓar bukatar belin ne a yayin zamanta na ranar Talata, 21 ga watan Janairun 2025
  • Alƙalin kotun mai shari'a Isa Aliyu, ya ɗage sauraron har zuwa ranar Alhamis, 23 ga watan Janairun 2025 don jin ba'asi kan buƙatar belin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wata babbar kotun jihar Kaduna ta sake ƙin bayar da beli ga tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin a lokacin, Nasir El-Rufai, Alhaji Bashir Sa’idu.

Kotun ta ba da umarnin a mayar da shi gidan yari bayan an gurfanar da shi a kan tuhume-tuhume guda 10 masu alaƙa da almundahana da sata.

Kotu ta ki ba ds belin Alhaji Bashir Saidu
Kotu ta hana Alhaji Bashir Saidu beli Hoto: Nasir El-Rufai, Bashir Saidu
Asali: Facebook

Ana tuhumar tsohon kwamishinan El-Rufai

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa

Lokacin da aka kawo ƙarar a gaban mai shari’a Isa Aliyu a ranar Talata, an karanta tuhume-tuhume 10 ga wanda ake tuhuma, wanda ya musanta dukkanin laifukan, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin tuhume-tuhumen, an zargi tsohon kwamishinan da sayar da $45m daga asusun gwamnatin jihar Kaduna, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 18.45, a farashi mai rahusa na N410 kan kowace dala.

Hakan ya saɓawa farashin kasuwa na N498 kan kowace dala, wanda hakan ya janyo asarar Naira biliyan 3.96 ga gwamnatin jihar.

A cewar masu shigar da ƙara, laifin ya faru ne a shekarar 2022, lokacin da Alhaji Sa’idu ke matsayin kwamishinan kuɗi a gwamnatin El-Rufai.

Tsohon kwamishinan El-Rufai ya nemi beli

Jaridar The Nation ta ce lauyan wanda ake tuhuma, M. I. Abubakar, ya sanar da kotun game da buƙatar neman belin da suke yi.

Ya ya roƙi kotun da ta bayar da belin Alhaji Bashir Sa’idu, duba da cewa ya riga ya kwashe kwana 21 a tsare tun bayan kama shi a ranar 2 ga watan Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun kashe farfesan jami'a a gidansa

Yayin da ya nuna cewa an shigar da buƙatar neman belin tun a ranar 16 ga Janairu, ya kafa hujjar cewa bayar da belin zai ba Alhaji Bashir Sa’idu isasshen lokaci wajen shirya kare kansa daga tuhume-tuhumen da ake masa.

Sai dai, Lauyan masu gabatar da ƙara, Farfesa Nasiru Aliyu, ya ƙalubalanci buƙatar belin, yana mai cewa doka ta tanadi a ba masu gabatar da ƙara kwana bakwai don yin martani kan buƙatar belin.

Bayan hutun mintuna 40, mai shari’a Isa Aliyu ya yanke hukunci cewa a ba masu gabatar da ƙara isasshen lokacin da doka ta tanada don gabatar da martani kan buƙatar belin.

Ya ɗage shari’ar zuwa ranar 23 ga Janairu, 2025 don sauraron buƙatar belin.

El-Rufai ya ziyarci tsohon kwamishinansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya kai ziyara ga tsohon kwamishinansa wanda yake tsare a gidan gyaran hali.

Nasir El-Rufai ya ziyarci Alhaji Bashir Sa'idu ne bayan an garƙame shi a gidan gyaran hali saboda zargin almundahanar kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng