"Akwai Illoli da Dama" TUC Ta Gargadi Gwamnati a kan Karin Haraji

"Akwai Illoli da Dama" TUC Ta Gargadi Gwamnati a kan Karin Haraji

  • ungiyar 'yan kasuwa ta kasa ta yi gargadi kan shirin karin VAT daga 7.5% zuwa 15% ga 'yan Najeriya
  • Shugaban kungiyar, Festus Osifo ya bayyana cewa talakawa za su fuskanci babbar matsala matukar aka yi haka
  • Ya shawarci gwamnati a kan kayyade iya kudin da za a rika karbar haraji a kansu, inda ya ba shawarar adadin kudin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kungiyar 'yan kasuwa (TUC) ta nuna adawa da shirin Gwamnatin Tarayya na karin Harajin Kayayyaki wato VAT.

Karin harajin ya na kunshe a cikin gyaran ƙudurorin harajin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Tinubu
TUC na son a sake duba kudirin gyaran haraji Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa TUC ta yi gargadin cewa wannan mataki na iya kara tsananta wahalhalun tattalin arziki da ’yan Najeriya ke fuskanta a yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta na ganin halin da 'yan kasa ke ciki a yanzu ya yi tsanani matuka saboda tsadar rayuwa, hauhawar farashi da karancin aikin yi.

Yadda gwamnati ta shirya kara haraji

Daily post ta ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta gabatar da shirin karin VAT daga 7.5% na yanzu zuwa 10%, 12.5%, har ma zuwa 15% a matakai daban-daban.

Kungiyar ta ce wannan mataki bai dace ba, kuma zai cutar da al’ummar da ke fama da hauhawar farashi, rashin ayyukan yi, da tsadar rayuwa.

Kungiyar TUC ta yi gargadi a kan haraji

Da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja ranar Talata, Shugaban TUC, Festus Osifo, ya jaddada cewa akwai bukatar a tsayar da adadin VAT a 7.5%.

Ya bayyana cewa wannan ya na da matukar muhimmanci wajen kare ’yan Najeriya daga karin matsin tattalin arziki.

Ya ce :

“Barin kaso na VAT ya kasance a 7.5% shi ne mafi alherin kasa. Kara shi a wannan lokaci zai kara wa iyalai da ’yan kasuwa nauyin da su ke dauke da shi sakamakon matsin tattalin arziki."

Kara karanta wannan

Kungiya ta gano sabuwar matsala a rabon harajin VAT, an gargadi gwamnonin Najeriya

“Da hauhawar farashi, rashin ayyukan yi, da tsadar rayuwa suna karuwa, karin haraji zai iya dakile ci gaban tattalin arziki da rage karfin sayen kayan amfanin yau da kullum.

TUC ta bukaci a sake duba dokar haraji

Kungiyar TUC ta bukaci a sake duba dokar da ke ba wa masu karamin karfi damar samun rangwame a haraji tare da kayyade kudin da haraji zai haiu kai.

Ya ce kama ya yi a haramtaharaji ga kudin da ya N800,000 zuwa N2.5 miliyan a shekara domin kara inganta rayuwar jama'a.

Ya ce;

“Wannan mataki zai kara kudin da za a kashe, ya farfado da ayyukan tattalin arziki, tare da ba wa ’yan Najeriya da ke fama da wahalhalu saukin rayuwa."
“Iyakar samun rangwamen haraji ya kamata a daga zuwa N2,500,000 a shekara. Wannan gyaran zai samar da sauki mai matukar muhimmanci ga masu karamin karfi, inda zai basu damar tsallake kalubalen tattalin arziki na yanzu.”

Kara karanta wannan

Karin kudin kira: NLC za ta saka kafar wando daya da gwamnatin Tinubu

TUC ta fara neman karin albashi

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar 'yan kasuwa ta TUC ta fara fafutukar neman gwamnatin Bola Tinubu ta sake kara albashin ma'aikata.

Shugaban kungiyar, Festus Osifo ya ce matakin ya zama dole duba da karin mastin rayuwa da ma'aikata su ke ciki, da kuma hauhawar farashi a kasuwanni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.