Bashir Ahmad Ya Jawo Jarfa, Nnamdi Kanu Ya Maka Shi a Kotu, Ya Nemi Diyyar N100bn

Bashir Ahmad Ya Jawo Jarfa, Nnamdi Kanu Ya Maka Shi a Kotu, Ya Nemi Diyyar N100bn

  • Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya kai karar Bashir Ahmad gaban kotu kan zargin bata masa suna ta hanyar kiransa 'dan ta'adda
  • Ahmad ya wallafa kalaman a shafin X yana cewa Nnamdi Kanu da masu goyon bayan sakinsa suna barazana ga kasa
  • Kanu na neman diyyar biliyan 100 tare da umarnin neman gafara a jaridun kasa guda uku don gyara barnar da ya yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kungiyar IPOB da aka tsare, Nnamdi Kanu, ya dauki mataki kan tsohon hadimin Muhammadu Buhari.

Kanu ya kai karar Bashir Ahmad kan kalaman batanci inda ya kira shi dan ta’adda a wani rubutu a kafar sadarwa.

Kanu ya shigar da korafi kotu kan Bashir Ahmad
Nnamdi Kanu ya maka Bashir Ahmad a kotu kan zargin kalaman batanci. Hoto: Bashir Ahmad, Biafra TV.
Asali: Facebook

Rubutun Bashir Ahmad da ya jefa shi a matsala

Bashir Ahmad ya wallafa a shafin X inda yake caccakar masu goyon bayan Nnamdi Kanu da sakinsa a matsayin makiyan kasa.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin rubutun, Bashir Ahmad ya ce ba zai goyi bayan sakin Kanu ba sai ya yi nadama tare da daina kalaman batanci ga Najeriya.

An wallafa kalamansa a wasu shafuka inda ya ce Kanu da masu goyon bayan sakinsa ‘yan kasa ne da ake gani a matsayin abokan gaba.

"Duk wanda ke goyon bayan sakin Nnamdi Kanu, wanda ake zargi da ta'addanci kuma shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, ya kamata a ɗauke shi a matsayin abokin gaba na wannan ƙasa."

- Bashir Ahmad

Korafin da Kanu ya shigar kan Bashir

The Guardian ta ruwaito cewa Ahmad ya ce ya kamata a sake Kanu ne kawai idan ya warke kuma ya daina ganin Najeriya da 'yan kasa a matsayin abin ki.

Kanu ya gabatar da karar ne ta hannun lauyansa, Barista Aloy Ejimakor, yana cewa a ranar 19 ga watan Janairu, 2025, Ahmad ya bata masa suna a X (Twitter).

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Kanu ya nemi diyyar biliyan 100a cikin karar da aka gabatar, yana cewa kalaman Ahmad sun zubar da mutuncinsa da bata masa suna.

Kanu ya zargi Bashir da zubar masa mutunci

A cikin takardar karar, ya bayyana cewa kalaman sun nuna shi a matsayin wanda aka tabbatar da aikata ta’addanci da rashin daraja ga rayukan mutane.

Ya kara da cewa wallafe-wallafen sun janyo masa zubar da mutunci a duniya, musamman a Najeriya, inda yake da masoya, abokan aiki da iyalai.

Kanu na neman kotu ta bayar da umarni ga Ahmad ya nemi gafara a jaridun The SUN da Daily Trust da The Guardian a shafi na gaba-gaba.

Haka zalika, ya nemi kotu ta umarci Ahmad ya biya N100bn daya a matsayin diyyar lalata masa suna da alfarma.

Turji: Kungiyar IPOB ta kalubalanci Bashir Ahmad

Kun ji cewa Kungiyar da ke rajin kafa kasar Biafra, IPOB ta yi magana kan hada Nnamdi Kanu da rikakken dan ta'adda, Bello Turji.

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

Kungiyar ta gargadi Bashir Ahmad bayan ya kwatanta Turji da Nnamdi Kanu kan ta'addanci a Najeriya.

IPOB ta ce Kanu dan Biafra ne wanda ke neman kafa kasar ta hanya mai kyau yayin da Turji ke ta'addanci karara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.