Mutane ba Su Dandara ba, An Sake Mamaye Tankar da Ta Faɗi ana Ɗibar 'Ganima'
- Kwanaki kalilan bayan fashewar tanka ya yi ajalin kusan mutum 100, mutane sun sake baibaye wata tanka da ta faɗi a jihar Neja
- Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa duk da an fara raɗe-raɗin tankar na ɗauke da man fetur, mutane ba su ji tsoron zuwa kwaso ganima ba
- Wata shaida da abin ya faru a gabanta, Fatimah Muhammed ta bayyana cewa tankar ta faɗi ne a kusa da gidan man AYM Shafa kuma man gyaɗa ta ɗauko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger - Ga dukkan alamu mutane ba su dandara ba, sun sake yi wa wata tankar dakon mai kawanya a jihar Neja kwanakin kaɗan bayan abin da ya faru a Dikko Junctio a jihar Neja.
Wata tankar mai da aka ce man gyaɗa ta ɗauko ta samu matsala ta faɗi a Bida da ke jihar Neja ranar Litinin, an ga mutane sun yi tururuwa suna ɗibar ganima.

Kara karanta wannan
"Ba haka ya kamata ba," Peter Obi ya kawo cikas a shirin haɗakar Atiku da Kwankwaso a 2027

Asali: Original
Premium Times ta rahoto cewa wannan al'amari na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan mummunar fashewar da ta auku bayan faɗuwar tanka a Dikko Junction.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da mutuwar mutane kusan 100 a wannan iftila'i, mutane sun manta sun sak efita ɗibar ganimar fetur da wata tankar ta sake faɗuwa a Bida duk a jihar Neja.
Yadda mutane suka sake kewaye tanka
Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna mutane suna kokarin debo mai, yayin da wasu kuma suke guduwa domin gujewa tashin gobara.
Wani mazaunin garin, Yinusa Jiya, ya shaidawa manema labarai cewa:
"Mutane ba su fargabar komai duk da an fara tunanin man fetur motar ke ɗauke da shi."
Mutane sun kwashe man gyaɗa a tankar
Amma wata ganau, Fatimah Mohammed, ta bayyana cewa tankar tana dauke ne da man gyada ba fetur ba.
“Motar ta fadi a kusa da gidan mai na AYM Shafa jiya (Litinin), kuma mutanen garin sun sace dimbin man gyadar da ke zubowa daga motar.”
Wannan lamarin ya zo ne kwanaki biyu bayan fashewar wata tankar mai da ta kashe mutane kimanin 98 a kusa da Dikko Junction da ke karamar hukumar Gurara a jihar Neja.
Rahotannin da Daily Trust ta tattara sun nuna cewa adadin wadanda suka mutu ya karu, sakamakon wasu daga cikin wadanda suka samu raunuka sun rasu a asibitocin da ake kula da su.
Wannan yanayi ya jawo damuwa, musamman ganin yadda mutane ke ƙara jefa kansu cikin haɗari duk da hadarin da ya faru kwanaki kadan da suka wuce.
Sai dai har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan wannan tanka da ta sake faɗuwa a Bida.
Ƴan Majalisa sun nuna damuwa da fashewar tanka
Kun ji cewa sanatocin Arewacin Najeriya sun gargaɗi mutane su gujewa zuwa kwaso mai idan tanka ta faɗi don kare rayukansu.
Sanatocin sun kuma nuna damuwa da takaicin mutuwar kusan mutum 100 saksmakon fashewar Tanka a Dikko Junction da ke jihar Neja.
Asali: Legit.ng