'Ku Mallaki Bitcoin': An Fadawa Tinubu Hanyar Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya

'Ku Mallaki Bitcoin': An Fadawa Tinubu Hanyar Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya

  • Hanu Agbodje ya bukaci Najeriya ta mallaki Bitcoin domin samun damar bunkasa tattalin arzikin kasa ta hanyar cryptocurrency
  • Darajar Bitcoin ya karu da kashi 116% a shekarar da ta gabata, yayin da ake hasashen zai kai dala 180,000 kafin karshen 2025
  • Kasar El Salvador ta samu nasara ta hanyar sanya Bitcoin a ya zama kudi a dokance, wanda ya karfafa yawon bude ido da tattali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani masanin fasahar kere-kere, Hanu Fejiro Agbodje, ya bayyana cewa cryptocurrency da kadarorin yanar gizo za su jawo arziki a duniya.

Hanu Agbodje ya bayyana cewa Najeriya na bukatar kafa wata lalitar ajiya domin mallakar Bitcoin, irin yadda ake da lalitar ajiyar zinare da dala.

Masani ya ba gwamnatin Tinubu shawara kan mallakar Bitcoin
Masani ya fadawa gwamnatin Najeriya amfanin mallakar Bitcoin a shekarar 2025. Hoto: @officialABAT/X, Westend61/Getty
Asali: Getty Images

Cryptocurrency zai taimaki 'yan Najeriya

Kimanin kashi 33% na al’ummar Najeriya suna zuba jari a cryptocurrency, inda Najeriya ke matsayi na biyu a duniya bayan Indiya inji rahoton Chainalysis.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa akwai hasashen cewa Najeriya za ta fuskanci wahalhalu a 2025, ana ganin masana’antar cryptocurrency za ta kawo sauki sosai.

Shekarar da ta gabata, darajar Bitcoin ta tashi da kashi 116%, sakamakon sha’awar da ke tattare da amincewa da Bitcoin ETFs.

Masani ya hango bunkasar Bitcoin a 2025

A wata hira da Channels Television, Agbodje ya ce hasashen 2025 shi ne harkar cryptocurrency a Najeriya zai kara samun ci gaba.

Agbodje ya ce:

“A 2025, kasuwa za ta kara girma, musamman yanzu da Donald Trump ya dawo mulki, Amurka za ta zamo mai goyon bayan crypto.”

Agbodje ya bayyana cewa, wannan zai haifar da dokoki da kirkirar sulallan crypto masu yawa, tare da kafa lalitar ajiyar Bitcoin a Amurka.

Ya ce Najeriya na bukatar jagorantar wannan fanni, musamman bayan kafa dokar crypto a shekarar da ta gabata.

Masani ya nemi Najeriya ta mallaki Bitcoin

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar barazanar Trump, Amurka ta toshe tallafin lafiya

A cewarsa, akwai bukatar gwamnati ta dauki matakan kara bunkasa masana'antar cryptocurrency a Najeriya.

Agbodje ya ce:

“A shekarar 2025, abin da nake fatan gani shi ne a kafa lalitar ajiyar Bitcoin ta musamman a Najeriya."

Ya kara da cewa Bitcoin zai iya kai dala $180,000 kafin karshen shekarar 2025, don haka wannan shekarar za ta yi tasiri a hada-hadar kudin intanet.

Agbodje ya ce Najeriya na bukatar mallakar Bitcoin domin zama cikin manyan kasashen da ke amfani da wannan damar ta amfani da kudin intanet.

Yadda kasashen duniya ke rike da Bitcoin

El Salvador ce kasar farko da ta fara amfani da Bitcoin a matsayin kudinta a dokance a 2021, wanda ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Wannan matakin ya inganta hada-hadar kudi ga talakawa, ya jawo zuba jari daga kasashen waje, sannan ya karfafa yawon bude ido da kashi 95%.

Wani rahoton CoinGecko na Agusta 2024 ya bayyana cewa gwamnatocin kasashe daban-daban suna rike da kashi 2.2% na Bitcoin a duniya.

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

Kasashe kamar Amurka, China, Birtaniya, El Salvador, da Ukraine su ne ke rike mafi yawan Bitcoin a duniya.

Bayan zaben Trump a watan Nuwamba, Bitcoin ya fara kai dala $100,000 a karon farko, inda darajarsa ta karu da kashi 51% cikin wata guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.