Yaki da Talauci: Gwamna Abba Ya Rabawa Mata Akuyoyi Domin Dogaro da Kansu
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ɗauki hanyar yaƙi da talauci da rashin aikin yi a tsakanin mutanen da yake mulka
- Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da shirin rabon dabbobi zagaye na biyu domin kiwo ga mata a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin za a raba akuyoyi guda uku ga mata 7,158 domin su dogara da kansu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ƙudiri aniyar yaƙi da talauci da bunƙasa dogaro da kai a tsakanin mata da matasa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da zagaye na biyu na shirin kiwon dabbobi.

Asali: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakin-Tofa, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya raba kayan dogaro da kai ga mata
Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewa shirin ya haɗa da rabon dabbobi ga mata a dukkanin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Mai magana da yawuun gwamnan ya ce an kawo shirin da nufin bunƙasa sana’ar kiwon dabbobi tsakanin mutane masu rauni.
A lokacin bikin ƙaddamar da shirin, Gwamna Abba ya sanar da cewa za a raba akuyoyi 7,158 ga mata 2,386 a wannan zagaye, inda kowace mace za ta samu akuyoyi uku.
Shirin ya kuma tanadi raba shanu 1,342 da raguna 1,822 ga mata da matasa a zagaye na gaba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na yaƙi da talauci ta hanyar kawo sababbin dabaru da shirye-shirye waɗanda za su amfani kowa.
Ya bayyana shirin a matsayin ginshiƙin ƙoƙarin da ake yi na ba mata da matasa hanyar dogaro da kansu.
Gwamna Abba Gida Gida ya yi gargaɗi

Kara karanta wannan
Oshiomhole ya cire tsoro, ya faɗi manyan ƙasa masu hannu a haƙar ma'adanai na haram
Gwamnan ya gargaɗi waɗanda za su ci gajiyar shirin kan salwantar da dabbobin ta hanyar da ba ta dace ba, yana mai jaddada muhimmancin yin gaskiya don cimma manufofin da aka ƙirƙiro shirin dominsu.
Shirin wanda ya kai darajar N2.3bn, ya nuna jajircewar gwamnati wajen kawo ci gaba mai ɗorewa, tare da ɗora al'ummomi kan hanyar dogaro da kansu.
Ta hanyar sanya mata da matasa cikin harkar kiwo, shirin zai bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ds rage dogara da samun agaji daga gwamnati.
Gwamna Abba ya koka kan ɓata sunan Fulani
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna damuwarsa kan yadda ake ɓata sunan al'ummar Fulani a Najeriya.
Gwamna Abba Kabor Yusuf ya bayyana cewa ko kaɗan bai dace ba yadda ake ɓata sunan Fulani tare da yi musu baƙin fenti a ƙasar nan.
Ya buƙaci Fulani da su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya ta hanyar haɗa kai domin tunkarar duk wata muzgunawa da ɓata sunan da ake yi musu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng