"Babu Kari": Hukumar NAHCON Ta Sanya Lokacin Kammala Biyan Kudin Hajjin 2025
- Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta tunatar da maniyyata dangane da biyan kuɗaɗen aikin Hajjin bana na shekarar 2025 domin zuwa ƙasa mai tsarki
- Hukumar NAHCON ta sanya wa'adin ranar, 31 ga watan Janairun 2025 ga maniyyata domin su kammala biyan kuɗaɗensu na aikin Hajji
- Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman ya nuna cewa maniyyata da suka gaza biyan kuɗaɗen kafin wanna lokacin, sai dai su haƙura da zuwa Saudiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta sanya lokacin kammala biyan kuɗin Hajjin shekarar 2025.
Hukumar NAHCON ta sanya wa’adin ranar 31 ga watan Janairun 2025 domin maniyyatan da ke da niyyar zuwa aikin Hajjin bana su kammala biyan kuɗaɗensu.

Asali: Facebook
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Usman, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton jaridar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me zai faru da waɗanda ba su gama biya ba?
A cewar shugaban na hukumar NAHCON, maniyyatan da ba suka gaza kammala biyan kuɗaɗensu kafin wa’adin, ba za su samu damar zuwa aikin Hajjin bana ba.
"Gwamnatin Saudiyya ta bayyana mana a yayin tarurruka daban-daban cewa wa’adin ranar 31 ga Janairu ta na nan daram ga duk masu niyyar zuwa aikin Hajji."
"Mun ji su, kuma mun tabbatar musu da cewa za mu bi wannan umarnin. Saboda haka, ina kira ga duk maniyyata su tabbatar sun kammala biyan kuɗaɗensu kafin wannan wa’adi."
"Ba za mu iya ba da tabbacin samun ƙarin lokaci ga duk maniyyatan da suka kasa kammala biyan kuɗaɗensu ba. Ko dai mutum ya biya kuɗin, ko kuma ya rasa damar zuwa Hajjin 2025."
"Wannan shi ne gargadin da muka samu daga hukumomin Saudiyya."
- Farfesa Abdullahi Usman.
NAHCON ta buƙaci a wayar da kan maniyyata
Haka kuma, Farfesa Abdullahi Usman ya yi kira ga hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan maniyyata.

Kara karanta wannan
Wani katafaren otal da kamfanoni 4 sun shiga gonar gwamnatin Kano, an ɗauki mataki
Ya kuma buƙaci su tabbatar da cewa an sanar da duk maniyyata su shirya don biyan kuɗinsu kafin wa’adin ranar 31 ga watan Janairun 2025.
Karanta wasu labaran kan hukumar NAHCON
- Hajjin 2025: Hukumar NAHCON ta shirya saukakawa maniyyata
- A karshe, an bayyana kudin kujerar aikin Hajjin 2024, Musulman Arewa za su biya N8.4m
- Hajj 2025: NAHCON ta fadi sunayen kamfanonin jirage 4 da za su yi jigilar alhazai
Gwamna Abba ya roƙi Tinubu kan Hajji
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa ƙoƙon bararsa ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Tinubu kan kuɗin Hajjin 2025.
Gwamna Abba ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta rage yawan kuɗaɗen da maniyyata za su biya domin zuwa sauke farali a ƙasa mai tsarki.
Abba Kabir ya nuna cewa ya kamata gwamnati ta yi duba da halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi domin ta sauƙaƙawa maniyyatan wajen rage kuɗaɗen zuwa aikin Hajjin na 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng