Gwamna Ya Rikita Ƴan Adawa, Manyan Kusoshi da Mambobi Sama da 40,000 Sun Koma APC

Gwamna Ya Rikita Ƴan Adawa, Manyan Kusoshi da Mambobi Sama da 40,000 Sun Koma APC

  • Manyan ƙusoshi da mambobi sama da 40,000 na jam'iyyun adawa daban-daban a jihar Katsina sun sauya sheka zuwa APC mai mulki
  • Gwamnan Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ne ya karɓe su hannu bibbiyu a wani taro da aka shirya a gidan gwamnati
  • Tsohon Shugaban PDP na Katsina, Rabiu Gambo Bakori, ya ce rikicin cikin gida a jam’iyyun adawa da nasarar Radda ne suka ja hankalinsu zuwa APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya karbi mambobi sama da 40,000 daga jam’iyyu adawa daban-daban da suka sauya sheka zuwa APC.

Gwamna Raɗɗa ya karɓi dubannin masu sauya shekar daga PDP da jam'iyyun adawa ne a wani taro da aka shirya a gidan gwamnatinsa da ke Katsina.

Malam Dikko Radda da masu sauya sheka.
Gwamna Radda ya karbi masu sauya sheka sama da 40,000 a jihar Katsina Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammed
Asali: Facebook

Sakataren watsa labaran gwamna, Ibrahim Kula Muhammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Talata.

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Radda ya kassara adawa a Katsina

A taron, Gwamna Dikko Radda ya bayyana matukar farin cikinsa kan wannan ci gaba da ya jawo manyan ƙusoshin siyasa zuwa jam'iyyar APC.

Ya yi alƙawarin cewa babu wanda za a nuna ma wariya a gwamnatinsa, inda ya umarci shugabannin APC a kowane mataki su jawo sababbin mambobin cikin harkokin jam'iyya.

Dikko ya ƙara da cewa shawarar da masu sauya shekar suka yanke na shiga APC wata babbar nasara ce a ƙoƙarin kawo ci gaba a Katsina.

Ya kuma yi kira ga sababbin ƴan APC da su haɗa kai da gwamnatinsa kuma su ba da gudummuwa a shirye-shiryen da aka ɗauko waɗanda suka fara kawo sauyi a Katsina.

“Shigowarku APC ya kara mana karfin gwiwa wajen aiwatar da manufofin da za su kawo ci gaba ga jihar Katsina. Za mu tabbatar da cewa an ba ku dama da martaba kamar sauran ƴan APC," in ji Gwamnan.

Kara karanta wannan

Bayan an nemi ya fice daga PDP, gwamna ya ɗauko mutum 8 ya ba su muƙamai

Manyan kusoshin da suka sauya sheƙa

Manyan ƙuoshin da suka sauya sheƙa zuwa APC daga tsagin adawa a Katsina sun haɗa da tsoffin mataimakin kakakin Majalisar dokokin Katsina, Alhaji Yakubu Idris Ɗan Chafa da Alhaji Hassan Rawayau.

Sauran sun hada da Alhaji Isah Hamisu Dandume daga jam’iyyar APP, Alhaji Musa Gafai, tsohon ɗan takarar Majalisar Wakilai a inuwar PDP da wasu tsoffin shugabanni a matakan jiha da ƙananan hukumomi.

Dalilin da ya sa suka zaɓi komawa APC

Da yake jawabi a madadin masu sauya shekar, tsohon shugaban PDP na Katsina, Alhaji Rabiu Gambo Bakori, ya faɗi dalilin da suka ja ra'ayinsu zuwa APC.

Ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyun adawa da kuma inhancin nasarar Gwamna Radda a zaben 2023 ne suka sa su yanke shawarar shiga APC.

Mai ba Gwamna shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo Gwajo, ya ce wadanda suka sauya shekar sun fito ne daga jam'iyyun daban-daban.

Kara karanta wannan

Gwamna Dikko Radda ya yi bayani bayan 'mika' mulkin Katsina ga PDP

Wani jigon APC, Usman Gide ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa wannan sauya sheka ta tabbatar da yadda jam'iyyar ta ƙara karɓuwa a wurin jama'a.

"Ba sai mun ce komai ba, mutane sun gani da idonsu, wannan alama ce da ke nuna jama'a sun yaba da salon mulkin APC a Katsina.
"Akwai sauran manyan kusoshin jam'iyyun adawa da za su shigo APC nan gaba," in ji Usman.

Ɗan takarar NNPP a Oyo ya koma APC

A wani labarin kun ji cewa ɗan takarar gwamna a inuwar NNPP a jihar Oyo ya watsar da jam'iyyar, ya koma APC domin shirin tunkarar zaɓen 2027.

Popoola Olukayode Joshua wanda aka fi sani da POJ a taƙaice ya sanar da barin NNPP zuwa APC a hukumance a ranar Alhamis, 16 ga Janairu 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262