Masu Gidan Mai Sun Fara Gyara Farashin Fetur bayan An Samu Karin Kudi

Masu Gidan Mai Sun Fara Gyara Farashin Fetur bayan An Samu Karin Kudi

  • Wasu gidajen mai a Legas da Kano sun gyara farashin litar fetur zuwa N970 da N1010, wanda aka alakanta karin farashin dakon mai
  • Gidajen mai na NNPCL sun samu cunkoso saboda saukin farashin N925 a Legas, yayin da aka samu layuka masu tsawo a wasu gidajen mai
  • Farashin danyen mai ya sauka a ranar Litinin kafin rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka, amma ya sake hawa daga baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Masu gidajen mai a Legas a ranar Litinin sun gyara farashin litar mansu bayan an samu rahoton kara farashin dakon kowace lita a kasar nan.

Jama'a sun fara bayyana ra'ayinsu a kan yadda aka samu karin farashin, inda matatar Dangote ta bude kofa wajen sanar da karin farashin a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

Bloomberg
An fara kara farashin lita fetur Hoto: Bloomberg
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa farashin danyen mai ya karu sosai makon da ya gabata, sai dai ya dan sauka a ranar Litinin, gabanin rantsar da sabon shugaban Amurka, Donald Trump.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Lahadi, matatar Dangote ta bayyana cewa karin farashin litar fetur na da alaka da sauye-sauyen farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

An fara gyara farashin litar mai

Zagayen wasu daga cikin gidajen mai ya nuna cewa wasu gidajen mai, ciki har da MRS, sun gyara farashin su zuwa N970 kowace lita.

A Kano, wasu da su ka zanta da Legit sun bayyana cewa an sayi litar man fetur a kan N1010 a gidan man Aliko, wanda shi wasu ke cewa shi ne mai dan dama-dama.

Wani mazaunin jihar ya ce;

"A ranar Lahadi na saya a kan N990, amma a Aliko an sayar da lita a kan N1010, kuma shi ne ma mai dan sauki-saukin."

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun sanar da saukar farashin fetur bayan karyewar abinci

Ra’ayoyin jama’a kan karin farashin fetur

Wani direba, Segun Joshua, ya bayyana cewa a gidajen NNPCL kawai ke sayarwa a mafi karancin farashi a yanzu, shi ya sa ake samun layuka masu tsawo.

Sai dai, dogayen layuka sun kuma bayyana a gidan mai na MRS da ke kan titin Ahmadu Bello, Victoria Island, Legas.

Farashin man fetur ya sauka a duniya

A ranar Litinin, farashin danyen mai ya sauka a kasuwannin duniya yayin da masu saye da sayarwa ke jiran rantsar da sabon shugaban Amurka, Donald Trump.

Farashin danyen mai a watan Maris ya ragu da 1.5%, inda ake sayar da ganga daya a kan $79.66, yayin da a watan Fabrairu ya sauka da 1.8% zuwa $76.46 kowace ganga.

Sai dai, bayan rantsar da shugaban a jiya, farashin danyen man ya dan karu zuwa $80.05 a kan kowace ganga.

Dangote ya kara farashin man fetur

A wani labarin, kun ji cewa matatar Dangote ta ce farashin fetur ba zai kai N1000 ba, a gidajen mai da su ka kulla alaka da shi duk da hauhawar farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Matatar ta alakanta karin farashin fetur da sauye-sauyen da ake samu a farashin danyen mai da kuma farashin dakon mai a kasuwannin duniya, amma duk da haka ya na kokarin sayarwa da sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.