Allah Mai Iko: Fitaccen Jarumin Kannywood, Adam A. Zango ba Shi da Lafiya
- Shahararren jarumin Kannywood, Adam A. Zango ya tabbatar da cewa yana fama da rashin lafiya tare da rokin al'umma da su sany shi da addu'a
- Jarumin ya kuma sanar da abokan sana'a, yan uwa da masoyansa cewa zai tafi hutun watanni uku daga gobe Asabar, 10 ga watan Oktoba, 2026
- Duk da Adam Zango bai bayyana kalar rashin lafiyar da take damunsa ba, ya ce hutun zai taimaka masa wajen kula da ka'idojin lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Fitaccen jarumim masana'antar shirya fina-finan Hausa da ke Arewacin Najeriya watau Kannywood, Adam A. Zango yana fama da matsalolin rashin lafiya.
Sakamakon haka ne Jarumi Adam Zango ya bayyana cewa zai tafi hutun watanni uku domin maida hankali kan dokoki da tsare-tsaren likotoci dangane da rashin lafiyar da yake fama da ita.

Source: Facebook
Adam A. Zango ya tafi hutun wata 3
Zango ta sanar da tafiya hutun na sa ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram da yammacin yau Juma'a, ga watan Oktoba, 2026.
Sai dai jarumin bai fayyace wace rashin lafiya yake fama da ita ba, amma ya nemi abokai yan uwa da masoyansa da su sanya shi a cikin addu'a domin ya samu lafiya.
Adam Zango ya bayyana cewa hutun wata ukun zai fara ne daga ranar Asabar, 10 g watan Oktoba, 2026 zuwa ranar 10 ga watan Janairu, 2027.
Bayanin da Adam Zango ya yi
A sakon da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Jarumi Adam A. Zango ya ce:
"Assalamu Alaikum! Ina mai sanar da dukan abokan sana,'a ta cewa zan tafi hutun watanni uku, daga ranar 10/11/2026 zuwa 10/02/2027 sakamakon duba lafiyata. Don haka ina buƙatar samun cikakken hutu da kulawa.
"Ina fatan za ku fahimci halin da nake ciki, tare da ba ni haɗin kai da goyon baya a wannan lokaci."
"Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba ni lafiya mai ɗorewa tare da dukkanin musulmai da suke jinya, Amin. Ina buƙatar addu'o'inku."
Mutane sun fara masa addu'a
Bayan wallafa wannan sanarwa a shafinsa, dubban mutane daga cikin masoyan Adam Zango da masu masa fatan alheri suka fara martani tare da yi masa addu'ar Allah Ya ba shi cikakkiyar lafiya.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama'a, ga su kamar haka:
Malam Adolucky Makarfi ya ce:
"Allah Ya ba ka ingantacciyar 'afiya ogah, Amen Ya Hayyu Ya Qayyum."
Ibrahim Dankanjiba ya ce:
"Masha Allah Allah Ubankiji Ya sa a tafi a sa'a, Allah ya baka lafiya mai kyakkyawar zuciya."
Aliyu Muhammad Shata ya ce:
"Allah Ya baka lafiya da nisan kwana masu albarka."
Yadda Adam Zango ya yi sabon aure
A baya, kun ji cewa jarumin Kannywood, Adam. A Zango ya yi sabon aure, inda rahotanni suka ce an daura auren ne da wata yar Jamhuriyar Nijar.
Wannna aure na jarumin na zuwa ne bayan aurensa da jarumar Kannywood, Maimuna Musa, wacce aka fi sani da Maimuna Pretty ya mutu.
Asali: Legit.ng

