Abin Tausayi: Mutane 5 Yan Gida 1 Sun Mutu daga Kamuwa da Wata Cuta a Kano

Abin Tausayi: Mutane 5 Yan Gida 1 Sun Mutu daga Kamuwa da Wata Cuta a Kano

  • Wani Iyali daya a Danbare New Layout da ke ƙaramar hukumar Kumbotso sun rasa yara biyar cikin kwanaki bakwai sakamakon wata rashin lafiya
  • Yaran, mata uku da maza biyu, sun mutu tsakanin 1 da 7 ga Oktoba, 2026 amma ana zargin rashin lafiyar na da alaka da cutar mashako
  • Hukumomin lafiya sun ce za su binciki lamarin, yayin da aka buƙaci jama’a su kai rahoton cututtukan da ake zargi da wuri kuma su nemi kulawar lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Wani iyali a Danbare New Layout da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Jihar Kano ya shiga jimami bayan rasuwar ’ya’yansu biyar cikin kwanaki bakwai.

Rahotanni sun nuna cewa yaran sun mutu ne sakamakon wata rashin lafiya da iyalan ke zargin cutar diphtheria watau mashako ce.

Kara karanta wannan

Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tribune Nigeria ta rahoto cewa yaran, waɗanda suka ƙunshi mata uku da maza biyu, sun rasu tsakanin 1 da 7 ga Oktoba, 2026, lamarin da ya jefa mahaifinsu, Alhaji Ibrahim Yusuf, da sauran ’yan uwa cikin babban tashin hankali.

A cewar bayanan da aka samu daga iyalin, lamrin ya fara ne ranar 1 ga Oktoba, lokacin da yara biyu, namiji da mace, suka mutu bayan fama da wata rashin lafiya da ake zargin diphtheria ce.

Yadda yara 3 suka rasu a Kano

Lamarin ya ƙara muni ranar 7 ga Oktoba, lokacin da wasu yara uku, mata biyu da namiji ɗaya, suka rasu. Rasuwar ta haifar da fargabar yiwuwar yaɗuwar cutar a cikin gidan da kuma sauran al’ummar Danbare.

Da aka tuntubi shugaban hukumar yaki da cututtuka ta Kano (KNCDC), Farfesa Muhammad Adamu Abbas, kan rahoton mutuwar yaran, ya yi alkawarin bincikar lamarin da kuma gano abubuwan da suka haddasa rasa rayukan.

Kara karanta wannan

Bayan hadarin Ondo, jirgin sojin Najeriya ya sake samun matsala a sama

Farfesa Abbas ya buƙaci mazauna jihar da su gaggauta kai rahoton cututtukan da ake zargi suna yaɗuwa zuwa cibiyar lafiya mafi kusa, tare da neman kulawar likita maimakon ƙoƙarin kula da marasa lafiya a gida.

Ya jaddada muhimmancin kai rahoto da wuri, gano cuta da kuma fara magani cikin lokaci wajen hana mace-mace da dakile yaɗuwar cututtuka irin su diphtheria.

Mahaifin yaran ya nemi agaji

Mahaifin yaran da suka rasu, Alhaji Ibrahim Yusuf, ya roƙi hukumomin lafiya da abin ya shafa da su gaggauta kawo masu dauki, gudanar da bincike kan mutuwar yaran tare da gano ainihin dalilin rashin lafiyar.

diphtheria
Yadda ake rigakafin cutar mashako (mun yi amfani d wannan hoton ne a matsayin nuni) Hoto: JUNI KRISWANTO/AFP
Source: Getty Images

Ya kuma yi kira da a ɗauki matakan kare sauran ’yan uwansa da suka rage da kuma sauran mazauna yankin daga yiwuwar yaɗuwar cutar.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, hukumomin lafiya ba su tabbatar da alaƙar da aka yi tsakanin mutuwar yaran da cutar diphtheria ba.

NCDC ta yi bayanin kan mashako

Kun ji cewa hukumar NCDC ta bayyana cewa galibin wadanda suka kamu da cutar mashako watau diphtheria ba su yi rigakafi ba.

Ta ce kashi 28 cikin 100 na wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar ba su san matsayin rigakafinsu ba, yana mai cewa yawancin wadanda suka mutu sakamakon cutar ba su yi rigakafi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262