Rayuwa Juyi Juyi: An Kwantar da Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, Zuma a Asibiti
- Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, mai shekaru 84, yana karɓar magani a asibiti bayan rashin lafiya
- Shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa likitoci sun fara kula da Zuma, yayin da babban likitan sojojin kasar ya samu bayani kan halin da yake ciki
- Jam'iyyar MKP ta ce Zuma yana cikin koshin lafiya, duk da rahotannin cewa an kai shi asibiti, bayan ya yi fice a siyasa tun bayan zaben 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
South Africa - Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, yana karɓar magani a asibiti bayan rashin lafiya, kamar yadda Shugaba Cyril Ramaphosa ya tabbatar ranar Juma'a.
Ramaphosa ya tabbatar da rahotannin cewa an kwantar da Zuma mai shekaru 84 a wani asibiti tun ranar Laraba, domin samun kulawar likitoci.

Source: Twitter
Yaushe Zuma ya jagoranci Afirka ta Kudu?
Zuma ya shugabanci Afirka ta Kudu daga shekarar 2009 zuwa 2018, lokacin da Ramaphosa ya karɓi ragamar shugabancin kasar, cewar TRT Afrika.
Ramaphosa ya ce
"Shugaba Jacob Zuma ba ya cikin koshin lafiya, kuma a yanzu likitoci sun fara ba shi kulawar lafiya."
An yada jawabin nasa ne ta gidan rediyon kasar, SABC, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Ramaphosa ya ce an kuma sanar da babban likitan sojojin kasar game da halin lafiyar tsohon shugaban kasar.
Ana masa fatan samun sauƙi cikin gaggawa
Wasu kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa an kai Zuma asibiti da motar daukar marasa lafiya ranar Laraba.
"Mun yi masa fatan samun sauƙi cikin gaggawa. Muna son ya samu lafiya, ya dawo tsaye, kuma ya ci gaba da yi wa al'ummar Afirka ta Kudu hidima ta kowace hanya."
- Cewar wata majiya
An ce an kai shi wani asibitin kula da lafiya da ke birnin Pietermaritzburg, a gabashin kasar.

Source: Getty Images
Jam'iyyar MKP ta yi magana kan lafiyarsa
Jam'iyyar Zuma, MKP, ta bayyana a wata sanarwa cewa yana asibiti domin duba lafiyarsa na yau da kullum, amma ba ta yi cikakken bayani ba.
Sanarwar ta ce:
"Mun tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya kuma yana cikin yanayi mai kyau."
Jacob Zuma na daga cikin manyan mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen fafutukar kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata, wato wariyar launin fata ta tsarin mulki, a Afirka ta Kudu.
Sai dai jam'iyyarsa ta African National Congress (ANC) ta tilasta masa yin murabus a shekarar 2018, kafin ya kammala wa'adinsa na biyu, cewar Punch.
Afirka ta Kudu: Yan Najeriya sun dauki makami
A baya, an ji cewa wasu 'yan Najeriya sun shirya kare kansu a kasar Afirka ta Kudu bayan wa'adin 30 ga Yunin shekarar 2026 da aka ba baki.
Kungiyoyin masu adawa da baƙi sun nemi a kori baki ɗaya baƙin da ke ƙasar, yayin da aka kashe wasu 'yan ƙasashen Afirka a hare-haren.
Gwamnatin Najeriya ta sake yin Allah wadai da hare-haren, tare da buƙatar hukumomin Afirka ta Kudu su tabbatar da tsaron 'yan kasarta.
Asali: Legit.ng

