Tinubu Ya Fadi Yadda za a Samu Bashin Gina Gidaje har Naira Miliyan 100
- Shugaba Bola Tinubu ya ce ’yan Najeriya da suka cika sharuda za su iya samun bashin sayen gida har Naira miliyan 100
- Za a biya bashin ne cikin shekaru 20, inda mai neman rancen zai fara da biyan kashi 10 cikin 100 na kudin gidan da ya saya
- Tinubu ya bayyana cewa sama da ’yan Najeriya 2,300 a jihohi 27 sun riga sun amfana da bashin Naira biliyan 160 ta wannan shiri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa ’yan Najeriya da suka cika sharuda za su iya samun bashin sayen gida har Naira miliyan 100.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata, inda ya ce gwamnatin tarayya ta bullo da shirin ne domin saukaka wa ’yan Najeriya mallakar gidaje maimakon ci gaba da zaman haya.

Source: Facebook
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Tinubu ya ce ana bayar da bashin ne ta hanyar asusun zuba jari a harkokin gidaje na MOFI, wanda ke da jarin Naira tiriliyan daya.
Yadda za a samu bashin
A cewar shugaban kasar, wanda ya cancanta zai iya samun bashin da zai biya cikin shekaru 20, bayan ya fara da bayar da kashi 10 cikin 100 na kudin gidan.
Tinubu ya yi misali da gidan da kudinsa ya kai Naira miliyan 10, inda ya ce mai son mallakar gidan zai fara da biyan Naira miliyan daya.
Punch ta rahoto cewa rahoton ya ce sauran kudin kuma zai biya ne kusan Naira 85,400 duk wata, har na tsawon shekaru 20.
Shugaban ya ce kawo yanzu, sama da ’yan Najeriya 2,300 a jihohi 27 sun samu bashin gidaje na jimillar Naira biliyan 160 ta wannan shiri.
FMBN za ta ba da bashin gidaje

Kara karanta wannan
Abin da ake zargi ya tabbata, jagoran ƴan bindiga ya faɗi dalilansu na ɗaukar makami
Tinubu ya kuma bayyana cewa an karfafa bankin bayar da lamunin gidaje na tarayya (FMBN) domin bai wa ’yan Najeriya da suka cancanta bashin har Naira miliyan 50.
Shugaban kasar ya ce bashin bankin zai kasance da ribar kashi shida cikin 100, kuma za a iya biya cikin shekara 30.
Ya kara da cewa ma’aikatan da ke cikin tsarin bayar da gudummawar fansho za su iya amfani da kashi 25 cikin 100 na kudin fanshonsu domin biyan kudin farko na sayen gida.

Source: Facebook
Haka kuma, ma’aurata za su iya hada takardun neman bashin tare domin kara damar samun kudi mai yawa.
Shugaban ya ce wadanda ba za su iya biyan bashin gida ba za su iya amfana da shirin Family Homes Fund, wanda ya samar da gidaje sama da 53 ga iyalai masu rauni da wadanda ba sa samun isasshen kulawa.
Tinubu zai kawo taki
A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya umarci hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki a masana'antar takin zamani su gaggauta shirye-shiryen samar da buhunan taki sama da miliyan uku.
An tsara raba takin ne ga manoma a fadin Najeriya gabanin fara noman rani, domin taimakawa wajen bunkasa samar da abinci da tabbatar da tsaron abinci a kasar.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da samar da kudi karkashin shirin Renewed Hope, wanda aka bullo da shi domin saukaka farashin taki, kara yawan amfanin gona da farfado da masana'antun hada takin zamani a Najeriya.
Asali: Legit.ng

