Takaitaccen tarihin babban darakta Aminu Saira

Takaitaccen tarihin babban darakta Aminu Saira

An haifi jarumi Aminu Saira a ranar 20 ga watan Afrilu. Wanda a yanzu yana da shekaru 38 kenan a duniya.

Aminu ya kasance shahararren marubuci, mai shirya fina-finai, sannan kuma darakta a Najeriya. Ya fito daga jihar Kano, Najeriya.

Ya karanci kimiyyar Qur’ani a makarantar kwalejin Aminu Kano. Da farko yana harkar kasuwanci ne, amma a shekarar 2006, zai ya sauya akalarsa inda y aba kamfanin Kannywood mamaki da aikinsa na farko wato fim din “Musnadi”.

Labari da dumi a kan Aminu Saira
Daraktan shirya fina-finan Hausa Aminu Saira Hoto: Dandalin Kannywood

KU KARANTA KUMA: Sababbin kyawawan hotunan Halima da Zahra BuhariSababbin kyawawan hotunan Halima da Zahra Buhari

Ya kasance mafi shahara gurin shirya fina-finai a dandalin Kannywood. Abokan aikinsa na sha’awar tsarin aikin sa, amincin sa, da kuma basirar sa. Bajintar sa ta fito ne bayan ya saki fim din san a “Jamila da Jamilu” a shekarar 2009. Wannan fim ya taimaka masa gurin samun lambar yabo da dama ciki harda darakta mafi inganci na shekarar a 2014.

Labari da dumi a kan Aminu Saira
Ya ciri tuta a matsayin daraktan daraktoci na kamfanin Kannywood Hoto: Dandalin Kannywood

A shekara ta 2016, an nada ma Aminu Saira kambun daraktan da ya fi ko wani darakta a Kannywood. Yana daya daga cikin masu biya sosai a tarihin masana’antar shirya fina-finai! Dada sanin labarin aminu Saira, tarihin sa, da kuma nasarorinsa a shafin mu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel