Babban Sarkin da ake Girmamawa a Najeriya Ya Fara Yi wa Tinubu Kamfen
- Yayin da ake maganar zaben 2027, Sarkin Ife, Oba Adeyeye Enitan, ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a bainar jama'a
- A cikin wani bidiyo da ya yaɗu a intanet, sarkin ya bayyana cewa Tinubu ya kawo sauye-sauye a Najeriya da ba a taɓa ganin irinsu ba
- Kalaman yabon da mai martaba Ooni ya yi wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu sun jawo 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabambanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Osun - Sarkin Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya tayar da kura a kafafen sada zumunta bayan ya yaba da sauye-sauyen da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar.
Ya yi magana ne a cikin wani bidiyo da ya bayyana a kafafen intanet ranar Juma'a, 10 ga Yuli, 2026 yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamar da ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement a Abuja.

Source: Instagram
Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ya nuna cewa sarkin ya bayyana cewa Tinubu "ya zo a shirye" kuma ya kawo sauye-sauye a Najeriya da ba a taɓa gani ba.
Sarkin gargajiya ya yabi Tinubu
A cikin bidiyon da ya bazu sosai a kafafen sadarwa, sarkin gargajiyar ya yabawa Bola Tinubu da cewa:
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zo cikin cikakken shiri, kuma sakamakon hakan a bayyane yake. Daga harkokin mulkin gwamnati zuwa ɓangaren masu zaman kansu, abin da ke faruwa a wannan ƙasa ba mu taɓa ganin irinsa ba."
Ooni ya kawo wasu muhimman alamomin tattalin arziki domin ƙarfafa ikirarinsa game da shugaban ƙasar, inda ya ce kasuwar hannayen jarin ƙasar nan na dab da kaiwa darajar kasuwa sama da Naira tiriliyan 140.
"Hasashe ya nuna a fili cewa Dala za ta daidaita, kuma ba za a samu wani abu da zai girgiza tsarin canjin kuɗinmu na ƙasashen waje ba."

Source: Facebook
Martanin da jama'a suka yi
Kalaman sarkin sun jawo suka a kafafen sada zumunta, lamarin da ya haifar da muhawara mai zafi tsakanin masu goyon baya da masu adawa.
Legit ta tattara wasu daga cikin martanin kamar haka:
isolatrg ya ce:
"Ooni Adeyeye! Ka faɗi gaskiya, Baba. Shugaba Tinubu yana aiki. Abin da kawai ke damuna shi ne ci gaba da hare-haren 'yan bindiga da rashin tsaro a ƙasar."
IamtherealOGL ya ce:
"Don Allah idan kuna magana kan sauye-sauyen, ku riƙa kawo misalai da yadda suka amfani talakan ƙasa. Idan duk waɗannan manyan mutane ne kawai suke jin labarin sauye-sauyen amma talaka bai ji ba, ta yaya za mu tantance aikin da aka ce shugaban ƙasar ya yi?"
AminJaman ya ce:
"Kabiyesi yana magana ne da salon hikima, don Allah kada ku fassara maganarsa ba daidai ba."
Ga bidiyon sarkin da Vanguard ta wallafa a X:
Ndume ya ba Tinubu shawara
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Ali Ndume ya ziyarci fadar shugaban kasa domin ganawa da Bola Ahmed Tinubu.
Ndume ya sanar da cewa ya ba shugaban kasar shawarar fitowa da kan shi yana magana da 'yan kasa maimakon turo hadiman shi a kusan ko yaushe.
Bugu da kari, sanatan ya sanar da cewa ya yi magana da shugaban a kan matsalolin tsaro, tsadar kayayyaki da sauran damuwowin Najeriya.
Asali: Legit.ng


