An Yi wa Tsohuwar Jaruma Mansura Isah Gwajin Miyagun Ƙwayoyi, Sakamako Ya Fito

An Yi wa Tsohuwar Jaruma Mansura Isah Gwajin Miyagun Ƙwayoyi, Sakamako Ya Fito

  • Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, ta ce an bukaci ta gabatar da sakamakon gwajin kwayoyi yayin neman wata dama ta aiki
  • Ta bayyana cewa sakamakon gwajin ya nuna ba ta amfani da kwayoyi, lamarin da ya sa aka yi mata tayin aiki da na zama jakadiya nan take
  • Mansurah ta bukaci matasa su guji amfani da miyagun kwayoyi, tana mai cewa hakan na iya hana su samun aiki da manyan damarmaki a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, ta bayyana yadda ta yi gwajin miyagun kwayoyi domin cika sharuddan neman wata dama, inda ta ce sakamakon ya bude mata wasu damarmaki.

Mansurah ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na sada zumunta, inda ta ce an bukaci ta yi gwajin kwaya da kuma gabatar da takardar shaidar gwajin kafin a iya bata aikin.

Kara karanta wannan

A yi hattara: Katsina, Sokoto da wasu jihohi 25 za su fuskanci ambaliyar ruwa

An yi wa Mansurah Isah gwajin miyagun kwayoyi, an gano ba ta cin ko goro.
Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta na jawabi a wani taro. Hoto: @mansurah_isah
Source: Instagram

An yi wa Mansurah Isah gwajin kwayoyi

A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, Mansurah Isah ta ce:

"Na nemi wata dama sai suka dage cewa suna bukatar na yi gwajin kwayoyi da kuma shaidar hakan. Ni lokacin ma ba na a Kano, don haka sai da na koma, na roke su su yi mun gwajin saboda na zo latti."

Mansurah ta ce ana gudanar da dukkan matakan gwajin a gaban wanda ake gwadawa, kuma ana samun sakamakon nan take domin kauce wa duk wata shakka ko zargin sauya samfurin gwaji.

"AlhamdulilLah, akwai mutane biyu ne kawai a gabana, don haka suka yarda za a yi mun. Nan take aka bani sakamako, babu wani batun jeka-ka-dawo, kuma a gabanka za a yi komai, dan ma kar ka ce an yi maka sharri ko ba naka ba ne."

- Mansurah Isah.

Sakamakon gwajin da aka yi wa Mansurah

Kara karanta wannan

An saki bidiyon bama baman da Putin ya harba babban birnin Ukraine

Jarumar ta ce ba ta yi mamakin ganin sakamakon ya nuna ba ta amfani da miyagun kwayoyi ba, domin ta san halayenta.

Sai dai ta ce wasu daga cikin ma'aikatan cibiyar sun nuna mamaki da farin ciki bayan sun ga sakamakon gwajin nata ya fito 'babu'.

Ta kara da cewa daya daga cikinsu ya tambaye ta ko goro ba ta ci? Inda ta amsa cewa masa da cewa ba ta tauna ko goro, kuma ba ta shan lemun kwalba ko na roba sai idan da dalili na lafiya.

Mansurah Isah ta yi kira ga matasa da su guji tu'ammali da miyagun kwayoyi.
Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah tana kallon madubi bayan ta yi kwalliya. Hoto: @mansurah_isah
Source: Instagram

Damar da Mansurah ta samu da sako ga matasa

Mansurah ta ce bayan sakamakon gwajin, an yi mata tayin aiki da kuma bukatar ta zama jakadiyar wasu shirye-shirye.

Ta ce ta amince za su yi aiki tare idan Allah ya so. A karshe, tsohuwar jarumar ta bukaci matasan Najeriya su nisanci amfani da miyagun kwayoyi domin kare makomarsu.

A cewarta, akwai kasashe da dama da kuma wasu ayyuka a Najeriya da ba za a iya samu ba sai an gabatar da sakamakon gwajin kwayoyi, tana mai jaddada cewa hakan na da muhimmanci ga duk wanda ke son gina kyakkyawar makoma.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta shiga batun ma'aikatar bogi, ta aika sako ga gwamnatin Tinubu

Matsayar Mansurah kan tallata Tinubu

A wani labari, mun ruwaito cewa, yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, 'yan siyasa na cigaba da bayyana manufosinsu domin samun goyon bayan jama'a.

Jarumar Kannywood, Mansurah Isah ta bayyana cewa za ta yi mai yiwuwa wajen tallata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Mansurah Isah ta sanar da cewa ita asalin 'yar jam'iyyar APC ce a Najeriya, inda ta ce ta shafe sama da shekara 10 tana tafiyar siyasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com