Za a Sha Shagali a Kannywood: M Shareef zai Auri Maryam Malika

Za a Sha Shagali a Kannywood: M Shareef zai Auri Maryam Malika

  • 'Yar fina-finan Kannywood, Maryam Muhammad wacce aka fi sani da Malika, za ta angwance da Abdulazeez Muhammad Shareef (Abdul M Shareef)
  • Za a ɗaura auren masu ne a ranar 27 ga watan Yuni, 2025 da karfe 1:00 na rana a Masallacin Zangon Daura da ke Unguwan Kaji, jihar Kaduna
  • Jarumar ta bayyana farin cikinta tare da godiya ga Allah da masoyanta, inda ta nemi addu’ar alheri daga jama’a yayin da ke shirin daura auren

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Lamari mai daɗi ya faru a masana’antar ta Kannywood, bayan da jaruma Maryam Muhammad (Malika) ta bayyana ranar da za a ɗaura auren ta da Abdul M Shareef.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da daura aure a tsakanin fitattun jaruman Kannywood a Najeriya.

Za a daura auren jaruma Malika
Za a daura auren Maryam Malika da Abdul M Shareef. Hoto: Maryam Malika
Asali: Facebook

Jarumar ta wallafa sanarwar ne a shafinta na Facebook inda ta bayyana cewa za a gudanar da ɗaurin auren a ranar 27 ga Yuni, 2025 a jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdul M Shareef da za a daura auren da shi, shi ne ɗan’uwan fitaccen mawaki Umar M Shareef, kuma sananne ne a kafafen sada zumunta.

Malika ta gayyaci mutane aurenta da M. Shareef

A cikin sakon da ta wallafa, Maryam Malika ta bukaci magoya bayanta su halarci daurin aurenta da za a yi a Kaduna:

Jarumar ta ce:

“Hakika komai lokaci ne, sauri ko hanzari ba na mutum ba ne. Ka nemi zabin Allah shi ne mafi kyau. Alhamdllh ina kara gayyatar masoyana a duk fadin inda suke.”

Ta cigaba da cewa:

“Alhamdulillah ina nuna farin ciki na ga Allah, ina kuma kara godewa masoyana a duk inda suke, masu min fatan alkairi da fadamin gaskiya a kan rayuwa.

"Yau dai ga rana da lokaci. Ubangiji ya ba ni iko, ku tayani addu'a.”
Maryam Malika ta gayyaci mutane zuwa aurenta
Maryam Malika ta gayyaci mutane zuwa aurenta. Hoto: Maryam Malika
Asali: Facebook

Wannan furuci na jarumar ya jawo dimbin taya murna da addu’o’i daga masoyanta a sassan duniya, ciki har da shahararrun 'yan fim da mawaka daga masana’antar Kannywood.

Abdul M Shareef ya yi godiya da fatan alheri

Angon Maryam Malika, Abdul M Shareef ya wallafa saƙon godiya a shafinsa na Facebook yana mai cewa:

“Alhamdulillah ina so na yi amfani da wannan dama na nuna godiya ga Allah da kuma ku masoyan mu maza da mata zuwa wurin daurin aure na. Nagode Allah ya bar zumunci.”

Daga cikin wadanda suka taya su murna akwai mashahuran mutane daga cikin masana’antar fina-finai da wakoki, da dama daga cikin mabiyansu a kafafen sada zumunta.

Wani rahoto da jaridar Leadership ta wallafa ya tabbatar da cewa za a daura auren jaruman a jihar Kaduna.

Aure tsakanin 'yan fim

A cikin ‘yan shekarun nan, an fara ganin yadda aure tsakanin jaruman Kannywood ke ƙara zama ruwan dare a masana’antar.

Wannan al’amari yana ƙara samun karbuwa daga jama’a da masoya, inda ake kallon hakan a matsayin alamar haɗin kai da fahimta tsakanin jarumai.

Masana’antar Kannywood dai na ɗaya daga cikin muhimman bangarori na nishadi a Arewacin Najeriya, kuma sabanin da ya gabata inda jaruman ke aure daga waje ko wasu sana'o'i daban, yanzu dai da dama daga cikinsu na auren juna.

Ana ganin hakan ya samo asali ne daga kusanci da ake yi da juna a wajen aiki, wanda ke ƙara haifar da fahimta, jituwa da soyayya tsakanin jarumai.

Daya daga cikin misalan da suka fi daukar hankalin jama’a shi ne auren jarumi Sani Danja da jaruma Mansura Isa a baya, wanda ya tayar da kura a kafafen sada zumunta, kodayake daga baya sun rabu.

Sabon labarin auren Maryam Malika da Abdul M Shareef ya sake bayyana yadda wannan al’ada ke karbuwa a cikin masana’antar, tare da nuna cewa soyayya na iya tsiro a inda ake aiki tare da juna.

Rarara ya auri Aisha Humaira a Maiduguri

A wani rahoton, kun ji yadda fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya auri Aisha Humaira a jihar Borno.

Manyan mutane ciki har da Sanata Barau Jibrin sun halarci daurin auren a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Daurin auren ya ja hankalin al'umma da dama musamman lura da cewa ba a fitar da wata sanarwar gayyatar daurin auren ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng