Adam A Zango da Wasu Jaruman Kannywood Sun Yi Hatsari a Hanyar Kano

Adam A Zango da Wasu Jaruman Kannywood Sun Yi Hatsari a Hanyar Kano

  • Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun tsallake rijiya da baya bayan gamuws da hatsarin mota a kan hanya daga Kaduna zuwa jihar Kano
  • Fitaccen jarumi Adam A. Zango na daga cikin wadanda suka tsira, tare da Kb Zango da wani da ake kira Oga Abdul, kamar yadda rahotanni suka tabbatar
  • Jarumi Abdul M Sherif shi tabbatar da haka inda ya wallafa sanarwa a Facebook, yana rokon addu’a, inda yake cewa lamarin ya zo da sauki sosai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa wasu daga cikin jaruman Kannywood sun gamu da hatsarin mota a kan hanyar Kaduna zuwa jihar Kano.

An tabbatar da cewa daga cikinsu akwai fitaccen jarumi, Adam A. Zango da wasu jarumai da suka hadu da iftila'in na hatsarin mota.

Adam Zango ya gamu da hatsarin mota
Adam A Zango da wasu jarumai sun yi hatsarin mota. Hoto: Adam A Zango.
Asali: Instagram

Daya daga cikin jaruman Kannywood, Abdul M Sherif ne ya tabbatar da haka a shafin Facebook a daren yau Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hatsarin mota ke laƙume rayukan mutane

Hatsarin mota na ci gaba da laƙume rayukan yan Najeriya da dama wanda ba za a iya misalta adadin waɗanda suke mutuwa ba.

Wasu masana na ganin hakan bai rasa nasaba da rashin kyawun hanyoyi wanda na daya daga cikin manyan dalilai na hatsarin mota.

Sannan akwai gangaci daga direbobin da ke tuki a manyan titunan Najeriya wanda su ma suna ba da gudunmawa.

Yan wasan Kano 21 sun mutu a hatsari

A kwanakin nan, wasu yan wasan jihar Kano sun gamu da mummunan hatsarin mota inda guda 21 suka rasa rayukansu.

Yan wasan Kano sun mutu ne a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar dawowa daga jihar Ogun bayan kammala gasar.

Rahotanni sun bayyana cewa ƴan wasan sun gamu da ajalinsu ne bayan sun halarci gasar wasanni wacce aka yi a jihar Ogun.

Wani jami'in hukumar wasanni ta Kano, Ado Salisu ya ce mutum 19 sun mutu nan take, yayin da biyu suka cika a asibiti.

Adam A Zango ya gamu da hatsarin mota
Adam A Zango da wasu jaruman Kannywood sun yi hatsari. Hoto: Adam A Zango.
Asali: Facebook

Jaruman Kannywood sun yi hatsarin mota

Da yake sanar faruwar hatsarin, jarumi Abdul M Sherif ya tabbatar da cewa lamarin ya zo sauki amma suna bukatar addu'o'in daga jama'a domin samun lafiya.

Sanarwar ta ce:

"Innalillahi, ku taya mu da addu'a, Allah ya ba Adam A Zango lafiya da Kb Zango da Oga Abdul. "
Da sauran jama'a da suka samu hatsari a hanyar Kano daga Kaduna, amma lamarin da sauki sosai."

Adam A Zango ya samu muƙami

A baya, mun ba ku labarin cewa shahararren jarumi kuma mawaki a masana'antar Kannywood, Adam A Zango ya zama babban darakta na gidan talabijin Qausain.

A cikin wata sanarwa da shugaban rukunin kamfanonin Qausain, Nasir Idris, ya fitar, an tabbatar da cewa nadin jarumi, Adam A. Zango zai fara aiki ne a nan take.

Hakazalika, rukunin kamfanonin Qausain ya nada Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin darakta mai zaman kansa domin ba da shawarwari na musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.