Barau Ya Yi Wa Rarara Gata a Aurensa, Jiga Jigan APC Sun Halarci Ƙayataccen Bikin
- Fitaccen mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara, ya angwance da Aisha Humaira, daya daga cikin mata masu taya shi amshin waka
- Bikin auren ya gudana a babban masallaci da ke Maiduguri, jihar Borno, tare da halartar manyan baki da dama daga fadin kasa
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya kasance wakilin ango, tare da tsohon gwamnan Katsina, Aminu Masari
- Mai taimakawa shugaban kasa wajen harkokin yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz, wanda mutumin Kano ne ya halarci daurin auren
- Bayan sanar da ranar bikin, jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta, musamman a yankin Arewacin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Fitaccen mawakin siyasa na jam’iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara ya zama ango a birnin Maiduguri.
Mawakin siyasar ya auri daya daga cikin jaruman Kannywood kuma abokiyar aikinsa, Aisha Humaira a Maiduguri a jihar Borno.

Asali: Facebook
Barau Jibrin ya zama wakilin mawaki Rarara
Sanata Barau Jibrin ya tabbatar da haka a Facebook inda ya ce an daura aurensu a wani masallaci da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno a yau ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bikin ya samu halartar mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, wanda ya kasance wakilin ango a wajen wannan gagarumin biki.
A cikin sanarwar, Barau ya ce:
"Na halarci bikin aure na shahararren mawaki, Dauda Kahutu Rarara da amaryarsa, Aisha Humaira, a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a yau.
"Ina mika gaisuwar taya murna ta musamman ga Rarara da Aisha Humaira, Allah Madaukakin Sarki ya albarkaci wannan aure da dukkan alheri na rayuwa.
"Bayan kammala bikin, Mai Girma Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya karbe ni tare da tawagata a fadar gwamnati, Allah ya ba da zaman lafiya."

Asali: Facebook
Jiga-jigan APC sun halarci bikin Rarara
Tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, da mai taimakawa shugaban kasa a harkar yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz, sun halarta.
Alhaji Rarara ya tabbatar da lamarin a shafinsa na Facebook inda ya yaba wa amaryarsa.
A cikin rubutun da ya yi, mawakin ya ce ba zai taba mantawa da wannan rana ba a rayuwarsa ta duniya.
Ya ce:
"Tantabara 'yar alkawari, Alhamdulillah yau rana ce ta farin ciki a wajena wacce ba zan taba mantawa da ita ba, ina alfahari da ke amaryata.
Auren Rarara ya jawo martani a kafofin sadarwa
Sanar da ranar auren mawakin ya jawo martani a kafafen sada zumunta duba da abin ya zo kaman ba zata.
Miliyoyin mutane musamman daga yankin Arewa sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari da ya jawo hankalin jama’a sosai.
Kalar auren da ya burge Rahama Sadau
Kun ji cewa jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta bayyana sha’awarta ga bikin jaruma Priscilla Ojo da fitaccen mawakin Tanzaniya, Juma Jux.
Sadau ta bayyana bikin a matsayin mai ban sha’awa, cike da abubuwan burgewa, kyau da kuma tsari mai kayatarwa tun daga farko har ƙarshensa.
Bikin ya ja hankalin mutane a kafafen sada zumunta, inda aka bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan bukukuwan da aka yi a 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng