Girma Ya Fadi: Malamin addini Ya Dirkawa Yarinya 'Yar Shekara 13 ciki

Girma Ya Fadi: Malamin addini Ya Dirkawa Yarinya 'Yar Shekara 13 ciki

  • Ana zargin wani fasto a cocin Christ Apostolic Church da ke jihar Ondo da yi wa wata yarinya ‘yar shekara 13 mai nakasa ciki
  • An damke faston tare da gabatar da shi gaban sarkin garin Oke-Gburowo, inda aka ce ya amsa laifinsa a bainar jama'a
  • Iyalan yarinyar da hukumomin tsaro na jihar sun bukaci a tabbatar da cewa an bi hanyar doka domin tabbatar da adalci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Wani fasto mai suna Peter James da ke jagorantar cocin Christ Apostolic Church, reshen Modebiayo a karamar hukumar Odigbo ta jihar Ondo, ya shiga hannu kan zargin lalata.

Rahotanni sun nuna cewa Fasto Peter James ya shiga hannu ne bisa zargin yi wa wata yarinya mai bukata ta musamman 'yar shekaru 13 ciki.

Jihar Ondo
An kama Fasto bisa zargin yi wa yar shekara 13 ciki. Hoto: Legit
Asali: Original

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa an kama fasto Peter James ne a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kama shi, mutane sun mika shi zuwa fada gaban sarkin yankin, Oba Oloja Moses Ogunmoyewa, domin amsa tambayoyi dangane da zargin da ake masa.

Wani makusancin iyalan yarinyar ya bayyana cewa faston ya amsa laifin a lokacin da aka gabatar da shi a fada, kuma sarki da wasu daga cikin jama’ar gari sun tabbatar da hakan.

Fasto ya amsa yi wa 'yar shekaru 13 ciki

Bayan da aka kai shi fada, an ce faston ya amsa cewa shi ne ya yi wa yarinyar ciki, inda aka rubuta ikirarin a gaban sarki da wasu dattawan gari.

Sai dai mahaifiyar yarinyar, Victoria Bernard, ta koka cewa faston ya fara musanta zargin saboda halin da ‘yarta ke ciki.

Ta bukaci gwamnati da kungiyoyi da kuma al’umma su shiga tsakani domin ganin an hukunta wanda ake zargi, ta hanyar doka da adalci.

Jami'an ‘yan sanda sun shiga lamarin

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaron Amotekun da ke Ore sun fara gudanar da bincike a kan lamarin domin gano gaskiya.

Haka kuma, cibiyar cocin da ke kula da reshen da faston ke jagoranta ta shiga tsakani, amma duk kokarin abokan aikinsa na ganin ya yarda da cewa ya amsa laifin ya ci tura.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Ayanlade Olayinka, ya tabbatar da samun rahoton lamarin. Ya ce an gayyaci wanda ake zargi domin amsa tambayoyi.

Olayinka ya kara da cewa babu shakka za a gudanar da bincike sosai kan lamarin, kuma rundunar ba za ta rufa wa kowa asiri ba domin ganin an tabbatar da gaskiya da adalci.

Yan sanda
'Yan sanda za su yi bincike kan faston da ake zargi da lalata. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Baban Chinedu na fuskantar barazana

A wani rahoton, kun ji cewa Baban Chinedu ya ce ya fara fuskantar bazarana bayan fara wa'azin kare addinin Musulunci da ya yi.

Tsohon dan wasan kwaikwayon ya ce tun da ya fara wa'azi yana kalubalantar malaman addinin Kirista aka fara barazanar kashe shi.

A cikin wani bayani da ya yi kan halin da yake ciki, Baban Chinedu ya ce ya daina kwana a gidan shi da ke birnin Kano saboda barazanar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng