Abin da Bangladesh Ta Ce da Saudiyya Ta Yanke Hukuncin Kisa kan Yan Kasarta
- Bangladesh ta nemi karin bayani daga Saudiyya kan kisan wasu ’yan ƙasarta biyu a Makka, bayan zargin aikata badala
- An kashe mutumin da matar ne bayan samun su da laifin aikata abin da hukumomin Saudiyya suka kira rashin ɗa’a a cikin masallaci
- Lamarin ya tayar da hankula a Bangladesh, inda sama da ’yan ƙasa miliyan uku ke zaune da aiki a Saudiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Dhaka, Bangladesh - Gwamnatin Bangladesh ta yi magana da Saudiyya ta yanke hukuncin kisa kan yan kasarta da aka kama zargin badala a masallacin Makkah.
Kasar ta nemi Saudiyya ta yi bayani kan kisan bayan jami’an Dhaka sun ce ba a sanar da su hukuncin kisan ba sai bayan an aiwatar da shi.

Source: Getty Images
An kashe mutumin da matar a ranar Larabar da ta gabata, bayan an same su da laifin aikata “aikin rashin ɗa’a” a cikin wani masallaci, cewar BBC.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali da sojojin Najeriya suka tare wasu matasa, suka harbe su har lahira
Me ma'aikatar cikin gida ta ce
Sai dai ma’aikatar cikin gida a Saudiyya ba ta bayyana takamaiman abin da suka aikata ba wanda shi ne ya jawo maganganu kan lamarin.
Gwamnatin Bangladesh na neman cikakken bayani kan laifin da ake zargin sun aikata da kuma yadda aka gudanar da shari’ar da ta kai ga yanke musu hukuncin kisa.
Jami’an gwamnati sun ce matakan da za su ɗauka na gaba za su dogara ne da amsar da hukumomin Saudiyya za su bayar.
Mataimakiyar ministar harkokin wajen Bangladesh, Shama Obaed Islam, ta ce ƙasarta ta tuntubi gwamnatin Saudiyya domin samun bayanai kan lamarin.
Ta ƙara da cewa gwamnati za ta yi nazarin matakan da za ta ɗauka, ciki har da yiwuwar dawo da gawarwakin mutanen gida, bayan samun bayanan da ta nema.
Islam ta kuma sake jaddada cewa gwamnatin Bangladesh za ta ci gaba da kare walwala da muradun ’yan ƙasarta da ke zaune da aiki a ƙasashen waje.

Source: Facebook
Halin da ake ciki a Bangladesh
Kisan ya tayar da hankula a Bangladesh, inda Saudiyya ke ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ma’aikatan ƙasar ke ƙaura zuwa domin neman aiki.
Fiye da ’yan Bangladesh miliyan uku ne ke zaune da aiki a Saudiyya, inda da yawa daga cikinsu ke gudanar da ayyukan da ba sa samun albashi mai yawa.
Ƙasashen biyu na da kusancin addini da tattalin arziki, lamarin da ya sa yanayin kisan ya zama babban abin damuwa ga jama’ar Bangladesh.
A cewar Ma’aikatar Cikin Gida ta kasar Saudiyya, an yanke wa mutanen biyu hukuncin kisa ƙarƙashin tsarin ta’azir, wani nau’in hukunci a shari’ar Musulunci da ke bai wa alƙalai damar tantance hukuncin da ya dace da wasu laifuka.
Ma’aikatar ta ce girman laifin da kuma keta alfarmar masallacin na daga cikin dalilan da suka sa aka yanke musu hukuncin kisa.
Tribune ta ruwaito cewa sunayen ’yan Bangladesh ɗin biyu sun bayyana cikin jerin fursunonin da Saudiyya ta bayar bayan ofishin jakadancin Bangladesh da ke Jeddah ya nemi jerin.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Yan daba ɗauke da makamai sun kewaye jigon APC, sun kashe shi nan take
An samu hadarin jirgin sama a Saudiyya
An ji cewa mutane biyu sun mutu bayan wani jirgin helikwafta na leƙen asiri mallakin rundunar tsaron ƙasar Saudiyya ya faɗi.
Kakakin ƙawancen Saudiyya da ke goyon bayan gwamnatin Yemen ya ce jami’an biyu da ke cikin jirgin sun rasu.
Lamarin ya faru ne yayin da rikicin Saudiyya da Houthi ke ci gaba, bayan sake komawar hare-hare kan jiragen ruwa.
Asali: Legit.ng
