An Rasa Rayuka bayan Jirgin Sama na Leken Asiri Ya Yi Hatsari a Saudiyya

An Rasa Rayuka bayan Jirgin Sama na Leken Asiri Ya Yi Hatsari a Saudiyya

  • Mutane biyu sun mutu bayan wani jirgin helikwafta na leƙen asiri mallakin rundunar tsaron ƙasar Saudiyya ya faɗi
  • Kakakin ƙawancen Saudiyya da ke goyon bayan gwamnatin Yemen ya ce jami’an biyu da ke cikin jirgin sun rasu
  • Lamarin ya faru ne yayin da rikicin Saudiyya da Houthi ke ci gaba, bayan sake komawar hare-hare kan jiragen ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudi - Majiyoyi daga kasar Saudiyya sun tabbatar da labarin faduwar jirgi mai saukar ungulu da ya yi hatsari a wani yanki.

Ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta domin tallafa wa halastacciyar gwamnati a Yemen ya bayyana ranar Lahadi cewa mutane biyu sun mutu.

Kakakin ƙawancen, Birgediya Janar Turki Al-Maliki, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa, cewar rahoton Al Jazeera.

Al-Maliki ya bayyana cewa jirgin helikwafta samfurin AH-6i, wanda rundunar tsaron ƙasar Saudiyya ke amfani da shi, ya yi hatsari a yankin Najran sakamakon wata matsalar fasaha.

Kara karanta wannan

Houthi: Iran ta yi magana kai kai hare hare masu zafi kasar Saudiyya

Ya bayyana cewa hatsarin ya yi sanadin mutuwar jami’ai biyu da ke cikin jirgin a matsayin ma’aikatan jirgin sama.

Tun da farko a ranar Lahadi, Al-Maliki ya sanar da cewa ƙawancen ya tare tare da lalata makamai masu linzami guda biyu da ƙungiyar Houthi ta harba zuwa Khamis Mushait.

Haka kuma, an tare tare da lalata wani jirgi marar matuƙi a sararin samaniyar yankin Riyadh.

Hukumar Tsaron Farar Hula ta Saudiyya ta sanar da cewa barazanar ta ƙare a biranen Abha da Khamis Mushait, da kuma babban birnin ƙasar, Riyadh.

A watan Yuli, yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a shekarar 2022 tsakanin ƙungiyar Houthi da gwamnatin Yemen ta rushe bayan Houthi ta zargi Riyadh da kai hari filin jirgin saman Sanaa domin hana wani jirgin saman Iran sauka a wurin.

Daga bisani, ƙungiyar ta sanar da kafa shingen hana zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa Saudiyya, a matsayin martani ga abin da ta kira shingen da aka sanya wa yankunan da take iko da su. Haka kuma, ta sake komawa kai hare-hare kan jiragen ruwan Saudiyya da wuraren samar da man fetur.

Kara karanta wannan

An kai ɗan Najeriya kotu kan ikirarin mallaka da shirin cefanar da jirgin sojoji

Yaƙin Yemen ya fara ne a shekarar 2014, lokacin da ƙungiyar Houthi ta ƙaddamar da gagarumin farmaki kan sojojin gwamnati tare da kwace ikon Sanaa, babban birnin Yemen, ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da talauci a duniya.

Tun daga shekarar 2015, Saudiyya ta jagoranci ƙawancen ƙasashe da ke goyon bayan gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita.

Karin bayani na tafe.....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.