Yadda Ƴan Kasuwa 2000 Suka Yi Asara, an Rasa Rayuka a Gobarar Tankar Mai a Edo.
- Gobara ta tashi a kasuwannin Oluku da ke Edo bayan fashewar tankar mai, inda mutane shida suka mutu, wasu 20 suka jikkata
- Hatsarin ya faru ne sakamakon mummunar hanya da ta sa tankar mai ta faɗi, lamarin da ya lalata shaguna da kayayyaki na biliyoyin nairori
- Gwamna Monday Okpebholo ya yi alƙawarin sake gina kasuwar Oluku tare da taimaka wa ’yan kasuwar da gobarar ta jefa cikin asara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Oluku, Edo - Akalla mutane shida sun mutu, yayin da wasu kusan 20 suka jikkata bayan fashewar tankar mai.
An tabbatar hadarin ta lalata kasuwanni biyu da shaguna da dama a Oluku, Ƙaramar Hukumar Ovia ta Jihar Edo.

Source: Facebook
Tankar mai: Yadda aka rasa rayuka a Edo
Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis, lokacin da wata tankar mai ɗauke da man fetur ta faɗi yayin ƙoƙarin juya wa zuwa hanyar Oluku da ke kan babbar hanyar Benin zuwa Legas, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Kaico: Mutane da dama sun mutu yayin da suka je ɗibar ganima jikin wata tankar fetur
Rahotanni sun bayyana cewa tankar ta faɗi ne bayan ta bugi wani mummunan ɓangaren hanyar.
Man da ke cikin tankar ya zube a kan hanya da wuraren da ke kewaye, lamarin da ya jawo hankalin mazauna yankin.
Sun fara kwashe man da ke zuba cikin robobi duk da gargaɗin jami’an tsaro, ciki har da sojoji, ’yan sanda, jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) da jami’an tsaron Jihar Edo.
An tattaro cewa daga baya masu tankar sun kawo wata tankar domin kwashe sauran man. A lokacin wannan aikin ne gobara ta tashi, ta cinye kasuwannin biyu da wasu shaguna kusan 30.
Gobarar ta lalata kayayyaki da kadarori da darajarsu ta kai biliyoyin nairori, a cewar ɗaya daga cikin masu kasuwannin. Motoci shida, tankokin mai biyu da wata motar dakon biskit su ma sun ƙone.
Kasuwannin da abin ya shafa mallakar Cif Osamede Adun, wanda aka fi sani da Bob Izua, da Kwamared Osaze Uwaifo, Okaighele na al’ummar Oluku ne.
Wasu ’yan kasuwa sun kuma yi zargin cewa ɓarayi sun wawushe kayayyaki daga shaguna yayin da gobarar ke yaɗuwa.

Source: Original
Martanin wasu yan kasuwa a Edo
Wata ’yar kasuwa mai suna Mrs Faith Julius ta ce kwanan nan ta sayi kayayyaki na sama da naira miliyan biyu, sannan ta ari wasu naira miliyan biyu domin sayen na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana, kwana biyu kacal kafin faruwar lamarin.
Mai ɗaya daga cikin kasuwannin, Cif Adun, ya roƙi gwamnatin jihar ta taimaka wa waɗanda abin ya shafa, cewar Vanguard.
Ya ce:
“Tuni abin ya faru. Muna roƙon gwamnatin jihar ta zo ta taimaka mana. Kuna iya ganin yadda gobara ta cinye dukiyoyi na biliyoyin nairori.”
Uwaifo ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya ƙara da cewa al’ummar yankin za ta nemi taimakon gwamnati domin tallafa wa ’yan kasuwar da suka yi asara.
Wata mai gidan sayar da iskar gas, Mrs Efe Adodo, ta ce gobarar ta bazu zuwa wajen gidanta, amma an shawo kanta da taimakon na’urorin kashe gobara.
An rasa rayuka bayan gobarar tankar mai
Mun ba ku labarin cewa an samu hadarin tankar mai a jihar Neja, lamarin da ya dagawa mazauna yankin Lapai hankali.
Rahoto ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu jami’ai a hukumomi daban-daban suna nan suna aikin tabbatar da tsaro.
Ana yawan samun hadurran manyan motoci a Najeriya, wannan na da nasaba da yaddaa titunan kasar ke lalacewa.
Asali: Legit.ng

