Obama Ya Kare Musulmar ‘Yar Majalisar Amurka da Trump Ya Taso Ta da Bincike

Obama Ya Kare Musulmar ‘Yar Majalisar Amurka da Trump Ya Taso Ta da Bincike

  • Barack Obama ya yi gargadi kan amfani da karfin ikon gwamnatin Amurka a kan masu adawa da shugaban kasa
  • Tsohon shugaban kasar ya ce lamarin Ilhan Omar na daga cikin abin da ake nuna matsin lambar da ake fuskanta
  • Obama ya dage cewa gwamnatin Trump na amfani da hukumomin tarayya wajen bibiyar abokan fada a Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

America - Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya ba Ilhan Omar kariya daga Donald Trump da ya matsa mata.

Ya zargi Shugaba Donald Trump da amfani da hukumomin gwamnatin tarayya wajen matsa wa 'yar majalisar wakilan Amurka.

Donald Trump, Ilhan Omar da Barack Obama a Amurka Hoto: Getty Images
Ilhan Omar da Rashida Tlaib suna sauraron Donald Trump a Majalisar Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A shafinsa na X, Barack Obama ya wallafa cewa an taso Ilhan Omar a gaba ne saboda sukar da take yi wa gwamnatin Trump.

Ya ce binciken da ake yi wa Ilhan Omar kan takardunta na shige da fice ya tayar da muhimman tambayoyi game da yadda ake aiki.

Kara karanta wannan

An dankaro wa Atiku tambayoyi masu zafi da ya nemi jin daga bakin ‘yan Najeriya

Obama wanda ya bar ofis a 2017 yana ganin ana amfani da ikon gwamnati a tursasa wa 'yan siyasa saboda ra'ayoyinsu a Amurka.

Ya ce bai kamata gwamnatin kasar ta zabi wasu mutane ta musguna musu saboda ra'ayoyinsu na siyasa ko kalaman da suke yi ba.

Wace ce Ilhan Omar a Amurka?

Ilhan Omar, wadda ke wakiltar jihar Minnesota a Majalisar Wakilan Amurka, ta kasance cikin manyan masu sukar Trump.

An haife ta a Somaliya, kuma ta koma Amurka tun tana yarinya, amma har yanzu wasu Amurkawa sukan yi mata gorin kasa.

A cewar Obama, abin da ake yi wa Ilhan ya saba wa muhimman ka'idojin tsarin dimokuradiyyar Amurka.

Meyasa ake binciken Ilhan Omar?

NBC News ta rahoto cewa a ranar 12 ga Oktoba, 2026, jami'an gwamnatin tarayya sun binciki gidanta da ke birnin Washington, D.C.

Mahukunta suna zargin cewa akwai rashin gaskiya a takardun ‘yar siyasar na shige da fice da samun takardar zama 'yar Amurka.

Jami'an sun kwace wayarta da wasu takardu, haka kuma sun aika da sammacin neman bayanai ga wasu daga cikin dangin Musulmar.

Kara karanta wannan

Lamari ya baci: Trump ya fatattaki mai magana da yawunsa kwana 5 da nada ta

Sai da ta musanta aikata ba daidai ba, tana mai cewa binciken na da alaka da siyasa kuma an shirya shi ne don ba ta tare da Trump.

Obama ya kare Ilhan da wasu a Amurka

Obama ya ce ta shiga Amurka tare da mahaifinta tana da shekara 12. Daga baya ta samu zama 'yar kasar Amurka ta hanyar mahaifinta.

Tsohon sanatan ya ce Ilhan ta zama yar kasar Amurka lokacin da take da shekara 17 da haihuwa.

Ya soki zargin da ake yi na cewa shekarunta sun kai 18 lokacin da mahaifinta ya samu zama ɗan kasa, don haka ya kamata ta nemi nata katin.

Ya kuma yi nuni da matakan da aka ɗauka a baya kan tsohon shugaban hukumar FBI, James Comey, da babban lauyan nan, Letitia James.

Obama ya yi gargaɗin cewa irin wannan hali na iya zama mummunan misali da sauran gwamnatoci za su iya amfani da shi a nan gaba.

Ya ce duk wani 'dan Amurka ya kamata ya damu da lamarin, ba tare da la'akari da ra'ayoyinsu kan Ilhan Omar ko matsayinta na siyasa ba.

Kara karanta wannan

Rigima ta shiga gwamnatin jihar Kano tsakanin wasu hadiman Abba Gida Gida

Trump yana matsa wa Ilhan lamba?

A nata bangaren, fadar White House ta karyata zargin cewa Trump na amfani da Ma'aikatar Shari'a wajen musguna wa abokan hamayya.

Fadar ta ce gwamnatin na mai da hankali ne kan tabbatar da bin doka da kuma kare lafiyar Amurkawa kamar yadda aka dauki alkawari.

CNN ta ce da aka tambayi shugaba Trump, ya sake sukar ta, ya kuma ce binciken da ake yi yana hannun ma’aikatar shari’ar kasar ne.

Ilhan Omar
Donald Trump, Ilhan Omar da Barack Obama a Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yar majalisa tana so a tsige Trump

Kwanaki aka ji 'yar majalisar Amurka, Ilhan Omar, ta fara kiraye-kirayen a tsige Shugaba Donald Trump saboda barazanar shafe kasar Iran.

Ta kuma bukaci a dawo da zaman majalisar wakilai don tattauna batun tsige shi da kuma amfani da Sashe na 25 na kundin tsarin mulkin Amurka.

Haka zalika, lhan ta nuna adawarta da takunkumin man da Trump ya kakaba wa kasar Cuba wanda ke sanya fararen hula shan wahala a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng