An rantsar da musulma ta farko yar kasar Somalia a matsayin yar majalisar dokokin Amurka

An rantsar da musulma ta farko yar kasar Somalia a matsayin yar majalisar dokokin Amurka

Wata budurwa musulma mai suna Ilhan Omar ta kafa tarihi a matsayin ta na musulma ta farko daga kasar Somalia data fara zama yar majalisar dokoki a kasar Amurka.

An rantsar da musulma ta farko yar kasar Somalia a matsayin yar majalisar dokokin Amurka
Ilhan Omar

Ita dai Ilhan yar gudun hijira ce daga kasar Somalia, an zabe ta ne don wakiltar al’ummar jihar Minnesota a majalisan wakilai na kasar Amurka. An haife ta a shekarar 1982, inda tayi hijira tare da iyayen ta zuwa Amurka a shekarar 1995 bayan barkewar yakin basasan kasar Somalia.

KU KARANTA:Al’ummar jihar Kwara sun tabbatar da amsan naira dubu biyar biyar da gwamnatin tarayya

Yar majalisa Ilhan tayi alkawarin wakiltar mutanen da ake nuna ma wariya. Ilhan ta lashe zabenta ne kwanaki kadan bayan zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zargi yan kasar Somali dake gudun hijira a jihar Minnesota da yada tsatstsauran ra’ayi.

Trump ya zargi wasu yan Somalia da ta’addanci inda yace “wasu daga cikinsu suna shiga kungiyar ISIS, kuma suna yada manufofin su”

Sai dai a wani labarin kuma, bincike ya nuna sama da kashi 50 na mutanen kasar Amurka basu gamsu da zababben shugaban kasar ba, Donald Trump.

Kalli bidiyon rantsar da Ilhan a nan:

Ku cigaba da bibiyan mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa/ ko a https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng