Lamari Ya Baci: Trump Ya Fatattaki Mai Magana da Yawunsa Kwana 5 da Nada Ta
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sallami sabuwar kakakinsa, Katie Zacharia, bayan kwanaki biyar kacal da nada ta kan mukamin
- Wasu masu ba Trump shawara sun ce Zacharia ba ta nuna kwarewa ko shirin da ake bukata wajen gudanar da muhimmin aikin ba
- Lamarin ya faru ne kasa da mako uku kafin zaben Amurka, a lokacin da Trump ke fuskantar matsin lamba kan yadda jam'iyyar Republican ke shirin zaben
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sallami kakakinsa ta fadar White House, Katie Zacharia, bayan kwanaki biyar kacal da fara aiki, sakamakon suka da ta fuskanta bayan fitowarta ta farko a gaban manema labarai.
Nadin Zacharia da sallamarta cikin kankanin lokaci sun jawo mamaki a tsakanin wasu jami'ai da masu ba shugaban shawara, wadanda suka nuna damuwa kan yadda aka bai wa wata da ba ta da isasshen kwarewa irin wannan mukami mai muhimmanci.

Source: Getty Images
Yadda Zacharia ta fara aikinta
Rahoton CNN ya nuna cewa Zacharia ta gudanar da taronta na farko da manema labarai a fadar White House na tsawon mintuna 14, inda ta fuskanci suka mai tsanani.
Bayan awa daya, ta kuma bayar da amsar da ta jawo tambayoyi lokacin da aka tambaye ta inda ta yi jarabawar zama lauya.
Duk da haka, Trump ya gaya mata cewa ta yi kokari yayin da suke cikin jirgin shugaban kasa zuwa Alaska, kamar yadda wani masani kan tattaunawar ya shaida.
Wannan ne karon farko da Zacharia ta hau jirgin Air Force One.
Masu ba Trump shawara sun damu
Wasu daga cikin masu ba Trump shawara sun ce Zacharia ba ta shirya yadda ya kamata ba, kuma ba ta nuna kwarewar da ake bukata wajen gudanar da aikin ba.
Wani daga cikinsu ya tambaya cikin mamaki ko akwai wanda ya tantance ta kafin a nada ta mukamin.
Rahoton ya ce jami'ai da masu ba shugaban shawara sun bayyana cewa ba a gudanar da cikakken tantancewa kafin nadin nata ba.
Dalilin da ya sa aka nada ta
Nadin Zacharia ya zo ne a lokacin da Trump ke nuna bacin rai kan karancin mutanen da ke kare shi a bainar jama'a, yayin da zaben Amurka ke gabatowa.
A cewar rahoton, shugaban ya nuna sha'awar nada wata mai biyayya gare shi wadda ta saba kare shi a kafafen talabijin, ba tare da yin la'akari sosai da sauran kwarewar da aikin ke bukata ba.

Source: Facebook
Sky News ta wallafa cewa an sallame ta ne bayan kwana uku da fara fuskantar suka, lamarin da ya kawo karshen zamanta a matsayin kakakin fadar White House cikin kwana biyar kacal.
Trump ya magantu kan Iran
A wani rahoton, kun ji cewa Donald Trump ya amince a wani gangamin siyasa a Youngstown, jihar Ohio, cewa Amurka ta wuce gona da iri wajen kashe shugabannin Iran.
Trump ya ce kashe shugabannin Iran ya sa Amurka ba ta san wadanda za ta tattauna da su ba, yana mai cewa rudani ya riga ya shiga lamarin.
Hakan na zuwa ne bayan shafe sama da wata 6 ana gwabza yaki tsakanin kasashen biyu ba tare da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin ba.
Asali: Legit.ng

