Pantami: PDP Ta Kafa Kwamitin Kamfen don Kwace Mulki a Hannun APC a Gombe

Pantami: PDP Ta Kafa Kwamitin Kamfen don Kwace Mulki a Hannun APC a Gombe

  • Jam’iyyar PDP reshen jihar Gombe ta sanar da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe
  • Tsohon jakada kuma Sanata Haruna Garba, Magayakin Gombe, zai jagoranci kwamitin, yayin da Ibrahim Hassan Dankwambo zai zama mataimakinsa
  • Jam’iyyar ta ce za ta fitar da sunayen mutum 2,000 da aka naɗa cikin kwamitocin da daraktoci daban-daban nan gaba kaɗan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Jam’iyyar PDP reshen jihar Gombe ta sanar da naɗa shugabannin kwamitin yaƙin neman zaɓenta na babban zaɓen shekarar 2027, yayin da take shirin fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen.

A sanarwar da jam’iyyar ta fitar, ta bayyana cewa tsohon jakada kuma Sanata Haruna Garba, wanda aka fi sani da Magayakin Gombe, zai zama shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da bidiyon rumbun makamai da ke karkashin kasa

Sheikh Pantami a taron PDP
Manyan PDP tare da Sheikh Isa Ali Pantami. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

PDP ta wallafa a Facebook cewa tsohon Gwamnan jihar Gombe, Sanata Dakta Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda aka fi sani da Talban Gombe, zai zama mataimakin shugaban kwamitin.

Haruna Garba zai jagoranci kwamitin

Sanarwar ta bayyana cewa Ambasada Sanata Haruna Garba (Magayakin Gombe) ne zai jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen na PDP a jihar.

A matsayinsa na mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Dakta Ibrahim Hassan Dankwambo (Talban Gombe) zai taimaka wajen jagorantar ayyukan kwamitin da kuma tsara dabarun gudanar da kamfen ɗin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta bayyana cewa sauran waɗanda aka naɗa za su riƙe muƙamai daban-daban domin tabbatar da gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓen a faɗin jihar.

Za a fitar da sunan mutum 2,000

Jam’iyyar PDP ta sanar da cewa ta naɗa mutum 2,000 da za su yi aiki a sassa daban-daban na kwamitin yaƙin neman zaɓen.

Sai dai ta ce ba ta fitar da cikakken jerin sunayen waɗanda aka naɗa ba tukuna, inda ta bayyana cewa za ta wallafa sunayen nan gaba kaɗan.

Kara karanta wannan

Maganar zargin kisan Kiristoci ya dawo yayin da zaɓen Najeriya ke ƙaratowa

Waɗanda aka naɗa za su yi aiki ne a daraktoci daban-daban, kwamitoci da kuma kwamitocin yaƙin neman zaɓe na ƙananan hukumomi 11 na jihar.

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami yayin shiga Gombe. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

A cewar sanarwar, sauran mambobin kwamitin za su riƙe muƙamai da ayyuka daban-daban domin tsara da kuma daidaita harkokin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a faɗin Gombe.

Wasu daga cikin wadanda aka nada:

01 SHUGABANCIN MAJALISAR YAKIN NEMAN ZABE NA JIHA

1. Sanata Haruna Garba (Magayakin Gombe) – Shugaban Majalisar Yakin Neman Zabe

2. Mai Girma Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo (Talban Gombe) – Mataimakin Shugaba

3. Farfesa Rabaran Usman Jidda Gelengu – Mataimakin Shugaba

4. Alhaji Aliyu Abubakar Deba (Sardaunan Deba) – Mataimakin Shugaba na Biyu

(5. Hon. Mohammed Dan'azumi Adamu (Madakin Pindiga) – Darakta-Janar

6. Hon. Danladi Garba Shongom – Mataimakin Darakta-Janar

7. Alhaji Usman Gurama – Mataimakin Darakta-Janar na Gombe ta Arewa

8. Magaji Kuji Pilam – Mataimakin Darakta-Janar na Gombe ta Tsakiya

9. Hon. Bulus Ma'Ori Esq – Mataimakin Darakta-Janar na Gombe ta Kudu

02 KWAMITIN BA DA SHAWARA NA JIHA

1. Dr. Abubakar Ali Gombe – Shugaba

Kara karanta wannan

An kwaye wa PDP, ADC zani a kasuwa kwanaki kaɗan bayan zuwa Atiku

2. Sanata Anthony Seyako Yaro – Mataimakin Shugaba na Musamman (Co-Chairman)

3. Dr. Rabaran Gerson Zubairu Laushege – Mataimakin Shugaba

4. Farfesa Sulaiman Muhammed – Sakatare

5. Alhaji Aliyu Hammadu (Kangiwan Gombe) – Mamba

6. Yarima Ibrahim Usman Deba – Mamba

7. Alhaji Muhammed Mustapha Ibrahim – Mamba

8. Farfesa Abubakar Gurama – Mamba

9. Farfesa Muhammed Danladi Musa – Mamba

10. Injiniya Aminu Ibrahim Jafar – Mamba

11. Alhaji Ibrahim Usman – Mamba

12. Alhaji Seyoji Abubakar – Mamba

13. Alhaji Ali Alhaji Deba – Mamba

14. Farfesa Usman Aliyu El-Nafaty – Mamba

03 SAURAN KWAMITOCI

1. Sashen Ayyuka da Gudanarwa

Hon. Sani Hassan S. Dogarai – Darakta

Hon. Hassan Muhammed Santana – Mataimakin Darakta

Alh. Adamu H. Abubakar (Sakataren Jam'iyyar PDP na Jiha) – Sakatare

2. Sashen Bincike, Dabaru da Tsare-Tsare

Dr. Abubakar Said Yagi – Darakta

Pantami ya shiga Gombe

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu matasa sun kunna wuta tare da toshe hanyar Jekadafari da ke kusa da gidansu Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a wani yunƙuri na hana Isa Ali Pantami shiga birnin Gombe.

Kara karanta wannan

Ana shirin zaben 2027: Gwamna Radda ya runtuma kora a gwamnatinsa

Lamarin ya faru ne lokacin da Pantami ke shigowa birnin domin halartar babban gangamin siyasa da PDP ta shirya, inda wutar tayoyin da aka kunna ta haifar da hayaƙi mai yawa.

Duk da toshe hanyar, ayarin motocin Pantami da ya ƙunshi daruruwan motoci ya samu damar wucewa zuwa wurin taron, yayin da wasu ’yan kasuwa suka rufe shaguna saboda fargabar barkewar rikici.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng