Rikicin ADC: "Hukuncin Kotu Bai Rusa Takarar Atiku a 2027 ba"
- Lauyan ADC, Kalu Kalu, ya ce babu wani sashe a hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu da ya soke takarar Atiku Abubakar
- Ya bayyana cewa abin da kotun ta soke shi ne duk matakai da ayyukan David Mark da Rauf Aregbesola tun daga 29 ga Yuli, 2025
- Rikicin ya samo asali ne daga ƙarar Nafiu Bala Gombe, wanda ya ƙalubalanci yadda shugabancin David Mark ya karɓi ragamar ADC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani lauya mai kare muradun jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Kalu Kalu, ya yi magana kan hukuncin kotu da ya soke shugabancin jam'iyyar.
Lauyan ya bayyana cewa hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke bai soke takarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.

Kara karanta wannan
Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027

Source: Facebook
Kalu ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026 yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels Tv.
Hakan na zuwa ne bayan an fitar da sahihin kwafin hukuncin kotun da ake ta ce-ce-ku-ce a kansa a ranar Laraba.
Lauyan ya zargi wasu mutane da ƙoƙarin jingina wa hukuncin umarnin da kotun ba ta bayar ba, yana mai cewa babu inda kotun ta bayyana soke takarar Atiku.
Abin da lauyan ya ce hukuncin ya ƙunsa
Kalu ya ce babu wani sashe a hukuncin da ya soke takarar Atiku Abubakar ko ta sauran ’yan takarar ADC.
“Hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu bai soke takarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar ranar 16 ga Janairu, 2027 ba ta kowace fuska. Babu wani sashe na hukuncin da ya soke takarar Atiku Abubakar ko ta sauran ’yan takarar jam’iyyar.” In ji shi.
Ya bukaci ’yan Najeriya da su karanta hukuncin da kansu, yana mai cewa wasu na fassara shi ta hanyar da ba ta dace ba.
A cewarsa, babban umarnin da aka bayar a hukuncin shi ne soke dukkan matakai da ayyukan da David Mark da Rauf Aregbesola suka gudanar tun daga ranar 29 ga Yuli, 2025.
Ya ƙara da cewa:
“Muna son a rubuta wannan a tarihi, bari duniya baki ɗaya ta je ta karanta hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu.
"Abin da za a iya samu daga hukuncin shi ne umarnin kotu na cewa duk matakai da ayyukan da David Mark da Aregbesola suka ɗauka tun daga ranar 29 ga Yuli, 2025, har zuwa yanzu, sun zama marasa amfani kuma ba su da wani tasiri. Amma wasu suna ƙara abubuwan da ba a bayyana ko ba a yanke hukunci a kansu ba.”
Yadda rikicin shugabancin ADC ya samo asali
A ranar 5 ga Nuwamba, Mai Shari’a Peter Lifu ya soke shugabancin ADC da David Mark ke jagoranta, tare da bayyana cewa duk matakan da kwamitin riƙon ƙwarya ya ɗauka ba su da inganci.

Kara karanta wannan
Matashin dan APC ya kama sunan Buhari, ya fadi rashin kyautawar da ya yi sa Tinubu a 2023
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Nafiu Bala Gombe, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, ya shigar.
Nafiu Bala ya ƙalubalanci yadda David Mark da sauran mambobin kwamitin suka karɓi shugabancin jam’iyyar bayan murabus ɗin tsohon shugaban ADC na ƙasa, Ralph Nwosu.
An ruwaito cewa hukuncin ya shafi tsarin da aka bi wajen fitar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, saboda kwamitin da Mark ke jagoranta ne ya shirya zaɓen fitar da gwani.
Fassarar da Kalu ya yi wa hukuncin ta ƙara fito da bambancin fahimta kan tasirin matakin kotun ga takarar Atiku a zaɓen 2027.

Source: Twitter
INEC na jiran kwafin hukuncin kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar INEC ta ce tana jiran samun sahihin kwafin hukuncin Babbar Kotun Tarayya kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC, kafin ta yanke shawarar matakin da za ta ɗauka.
Hukumar ta bayyana cewa sashen shari’arta zai nazarci hukuncin tare da ba ta shawarar matakan da suka dace bayan ta karɓi takardar.
Asali: Legit.ng
