Wike Ya Shirya Kawo Tinubu Ƙarfi da Yaji a 2027, Ya Yi Abin da ba a Taɓa Yi ba
- Nyesom Wike ya umarci mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu a Rivers su riƙa jawo sabbin masu zaɓe biyar a kowace rana
- Ministan ya sanya burin samo wa Tinubu ƙuri'u miliyan uku a jihar Rivers a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Gwamna Siminalayi Fubara ya ce sabon kwamitin ya fi wanda ya yi aiki a zaɓen 2023 girma da ingantaccen tsari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Rivers - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu a jihar Rivers.
Ministan ya umurci mambobinsa su riƙa jawo aƙalla sabbabin masu zaɓe biyar a kowace rana domin samun nasara a 2027.

Source: Facebook
Bukatar Wike ga mambobin kwamitin kamfen
Wike ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da kwamitin a ranar Alhamis, inda ya kuma sanya wa mambobinsa burin samo wa Tinubu ƙuri'u miliyan uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan
Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro
Ministan ya buƙaci mambobin kwamitin su mayar da hankali kan aiki tukuru, haɗin kai da gudanar da yaƙin neman zaɓe bisa muhimman batutuwa, ba tare da ɗaukar hankalinsu kan rikice-rikicen da suka shafi naɗe-naɗen mukamai a kwamitocin ba.
Ya ce yana sa ran zuwa ranar Litinin za a kammala jerin sunayen shugabanni da mambobin ƙananan kwamitoci domin su fara gudanar da ayyukansu.
Wike ya bayyana cewa samun nasara a Rivers ba abin da yake shakkunsa ba ne, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda za su tabbatar da samun ƙuri'u miliyan uku da suka sanya a gaba.
Ya bayyana cewa burin ƙuri'u miliyan ukun ya samo asali ne daga tattaunawarsa da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda ya tambaye shi adadin masu zaɓen da aka yi wa rajista a jihar.

Source: Facebook
A cewarsa, ya shaida wa Akpabio cewa jihar na da sama da masu zaɓe miliyan uku, inda ya amince za su yi ƙoƙarin samar da adadin ƙuri'un ga Tinubu.
Shawarar Wike ga mambobin kwamitin
Wike ya kuma bukaci mambobin kwamitin da su ɗauki naɗin da aka yi musu a matsayin damar yi wa ƙungiyar Rainbow Coalition aiki, tare da jan hankalinsu kan muhimmancin haɗin kai da ladabtarwa.
Ya yi nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Oba Rasheed Ladoja, ya bayyana goyon bayansa ga Rainbow Coalition lokacin da shugabannin PDP suka kai masa ziyara ta musamman.
A nasa ɓangaren, Gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa sabon kwamitin ya fi wanda ya yi aiki a zaɓen 2023 girma, faɗi da kuma ingantaccen tsari.
Fubara ya ce mutanen da a baya suke adawa da juna a siyasa sun haɗa kai domin yin aiki tare wajen ganin an samu nasarar Tinubu a zaɓen 2027.
Ya kuma tabbatar wa waɗanda ba su samu mukamai a babban kwamitin ba cewa za a ba su dama a ƙananan kwamitocin da za a kafa, cewar Punch.
Gwamnan ya gargaɗi mambobin kan guje wa munafunci da yi wa juna zagon ƙasa, inda ya bukaci kowa ya kasance mai gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da aikin da aka ɗora musu.
Tinubu ya yi magana da Fubara
A wani labarin, an ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa Gwamna Siminalayi Fubara cewa ba zai yi nadamar amincewa da sasancinsa kan rikicin siyasar Rivers ba.
Tinubu ya yabawa Fubara bisa balaga, fahimtar juna da mutunta shugabanni, yayin da ya kuma jinjinawa Nyesom Wike kan ayyukan raya ƙasa.
Gwamna Fubara ya yi alkawarin cewa Rivers za ta samar wa Tinubu ƙuri'u miliyan uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Asali: Legit.ng

