An Dankaro wa Atiku Tambayoyi Masu Zafi da Ya Nemi Jin daga Bakin ‘Yan Najeriya

An Dankaro wa Atiku Tambayoyi Masu Zafi da Ya Nemi Jin daga Bakin ‘Yan Najeriya

  • Alhaji Atiku Abubakar ya kirkiro dandalin Ask AA domin masu son yi masa tambayoyi kai-tsaye cikin sauki
  • An aika tambayoyi masu zafi, amma wasu amsoshin ‘dan takaran shugaban kasar na ADC ba su gamsar ba
  • Atiku Abubakar ya iya bada amsar abin da zai iya, a wasu wuraren kuma ya yi ‘yan dabaru na 'yan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Atiku Abububakar ya bude kofa a yi masa tambayoyi yayn da ya dage wajen takarar shugaban kasa a karkashin ADC.

Jama’a suna ta amfani da damar da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bada ta dandalin Ask AA a yanar gizo.

Atiku
Atiku Abubakar mai neman takara a ADC zaune a gida Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Dandalin Ask Atiku da aka fito da shi

Wani bincike da Premium Times ta gudanar a kan amsoshi 100 da aka wallafa a dandalin ya nuna Atiku bai bada amsa da kyau ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ziyarci Yari da labaran karya da suka yi ta yawo a makon da ya wuce

Amsoshin ba su kunshi cikakkun bayanan da aka nema ba, musamman kan kadarorin gwamnati, silar kudi da alkawuran siyasa.

Ana amfani da AI wajen amsa wasu tambayoyi, wadanda suka gagari fasahar kuma sai su je teburin Atiku domin ya amsa da kan shi.

Wasu tambayoyin da aka yi wa Atiku Abubakar

Wani ya jefa tambaya game da sunayen manyan kadarorin gwamnati da aka saida kacin da Atiku ke sa ido a gwanjon kayan hukuma.

Ya bukaci jin sunayen wadanda suka saye kayan da farashin da aka sayar masu, dandalin bai bayar da wadannan bayanai ba.

Maimakon haka, an umurci mai tambayar da ya tuntubi Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE) da alhaki yake hannunta.

Wata tambaya kuma ta nemi sanin ko Atiku zai bayyana cikakken bayanan kadarorinsa ga jama’a, maimakon sai ya yi kauce-kauce.

Ya ce bai taba guje wa bayyana kadarorinsa ba, amma bai ce zai yi wannan bayani ga jama’a ba, za a bar maganar ne wajen hukuma.

Kara karanta wannan

'Na ga fuskar yarinyata,' Makahon da ya shekara 27 babu idanu ya dawo yana gani

Daya daga cikin manufofin Atiku da aka yi tambaya a kan sa shi ne shirin tallafa wa farashin man fetur da aka tace a cikin gida.

An tambayi dandalin ko nawa shirin zai lakume a duk shekara da kuma inda za a samo kudin ta yadda fetur zai yi araha a kasar.

Amsar shi dai ta ambaci sayar da danyen mai a cikin gida, hanyoyin daidaita kudin gwamnati da sha’anin farashin kayan mai.

Amma bai iya bayyana adadin kudin ba ko kuma kiyasin abin da za a kashe a shekara.

Sai dai amsar tambayar da ta shafi yadda za a hana zamba a shirin tallafin ta fi fayyace matakan, a nan kila ya fi burge jama’a.

An kuma yi tambayoyi kan shekarun Atiku da kuma yiwuwar tsawon lokacin da zai yi a kan mulki idan ya zama shugaban kasa.

Wani matambayin ya kuma tambayi ko tsohon mataimakin shugaban kasar zai yi wa’adi daya kacal idan aka zabe shi a 2027.

Amsar ta ce:

“Wa’adi na biyu ba hakki ne da mutum zai samu kai tsaye ba.”

Kara karanta wannan

Lamari ya baci: Trump ya fatattaki mai magana da yawunsa kwana 5 da nada ta

Sai dai amsar ba ta zama cikakken alkawarin cewa zai yi wa’adi daya kacal ba, tana nuna sai shugaba ya yi aiki sannan zai zarce.

A shafin X, an ji wasu suna neman jin ta yadda babban 'dan siyasar ya samu arziki mai yawa.

Nasir El-Rufai ya ga ta kan shi a kotu

Labari ya zo kwanakin baya cewa wani shaidan DSS a Kotu ya ce Nasir El-Rufai sun tanadi $600, 000 da nufin hana binciken EFCC.

Segun Kayode ya shaida wa alkali cewa sun yi amfani da fasahar zamani wajen nadar muryar mutane, yanzu ake amfani da su a kotu.

Lauyan tsohon gwamnan ya kalubalanci shaidar da aka bayar da aka shafe awanni 9 ana zama a kotu amma bi yi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng