Musulunci Ya Kara Karfi a Turai, za a Fara Bin Tsarin Shari'a a Birtaniya

Musulunci Ya Kara Karfi a Turai, za a Fara Bin Tsarin Shari'a a Birtaniya

  • Jami’o’in Biritaniya sun fara tallata shirin bashin karatu mara ruwa da ke bin tsarin addinin Musulunci ga ɗalibai Musulmi da sauran al'umma
  • Ana kyautata zaton za a fara amfani da wannan sabon tsarin a shekarar karatu mai zuwa ta 2026-27 don ba da damar karatun jami'a cikin sauƙi
  • Wasu sun soki matakin, inda 'yan hamayya irin su Suella Braverman suka ce tsarin zai haifar da bambanci da kuma samar da korafi a cikin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

London – Jami’o’i da dama a Biritaniya sun fara tallata wani sabon tsarin bashin karatu mara ruwa wanda yake dacewa da koyarwar addinin Musulunci domin amfanin ɗalibai Musulmi da ma sauran jama’a.

Wannan tsari an tsara shi ne domin ba wa ɗalibai Musulmi damar samun ilimin jami’a cikin sauƙi ba tare da sabawa dokokin addininsu da suka haramta karɓa ko biyan ruwa ba.

Kara karanta wannan

Abu ya gagara karewa: Gwamna Radda ya fadi yadda zai dakile matsalar tsaro

Andy Burnham na Birtaniya
Firaministan Birtaniya, Andy Burnham. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Telegraph ta rahoto cewa a ƙarƙashin tsarin, kuɗin da ɗalibai za su riƙa biya ba za su koma ma'ajiya ta gaba ɗaya ta gwamnati ba, a'a za a adana su ne domin sake bai wa sauran ɗalibai masu buƙatar bashi.

Za a bi tsarin Musulunci a Birtaniya

Tsarin yana amfani da dabarun hada-hadar kuɗi na Musulunci da ake kira Takaful, inda maimakon biyan kuɗin ruwa a kan ainihin kuɗin da aka karɓa, ɗalibai za su riƙa biyan gudunmawa ta musamman wadda za ta taimaka wa shirin a nan gaba.

Irin waɗannan jami'o'i kamar Bristol, Leeds, Newcastle, da University College London sun fara sanar da ɗalibai cewa bashin zai kasance a shirye a shekarar karatu ta 2026-27.

Maganar shirin ta samun kariya daga ma'aikatar ilimi sakamakon wani bincike da ya nuna kusan kashi 80 cikin ɗari na ɗalibai Musulmi a ƙasar na fuskantar matsin lamba kan amfani da tsarin bashi mai ruwa.

Kara karanta wannan

An kara wa jami'an INEC albashi da alawus yayin da ake shirin zaben 2027

Masu sukar tsarin a Birtaniya

Ita kuwa mai magana da yawun jam'iyyar Reform kan harkokin ilimi, Suella Braverman, ta soki matakin matuka.

Ta bayyana cewa:

“Wannan tsarin ya saɓa wa dabi'un Biritaniya kuma yana haifar da tsari mai fuska biyu a fannin ilimi da rarrabuwar kai a al'umma. Shirin da jam'iyyar Labour ta kawo yana tabbatar da cewa suna da ma'auni biyu a dukkan fannonin rayuwa a Biritaniya.”
Kusa da jami'ar London a Birtaniya
Dalibai na wucewa kusa da jami'ar London. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Braverman ta ƙara da cewa gwamnati ta biya ƙungiyar Islamic Finance Council UK fiye da £365,000 domin tsara wannan tsarin, inda ta ce ’yan ƙasa za su ci gaba da ɗaukar nauyin kuɗin idan har ɗalibai ba su sami damar biya ba.

An shiga watan Jumada Sani

A wani labarin, kun ji cewa Fadar Sarkin Musulmi ta sanar da cewa Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, ita ce ranar farko ta watan Jumada Sani na shekarar 1448 bayan hijira.

Fadar ta bayyana cewa ba a samu rahoton ganin jinjirin watan Jumada Sani daga kwamitocin duban wata na sassan Najeriya ba a ranar Litinin.

Sakamakon haka, ranar Talata, 10 ga Nuwamba, ta zama ranar cika kwana 30 na watan Jumadal Ula, wanda ya sa Laraba ta zama farkon sabon watan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng