Mutuwa Ta Ratsa Gwamnatin Dauda Lawal a Zamfara, Kwamishina Ya Rasa Yana da Shekara 50
- Kwamishinan Kasuwanci na Zamfara, Tasiu Musa Shinkafi, ya rasu ranar Laraba a Kaduna bayan fama da gajeriyar rashin lafiya
- Gwamna Dauda Lawal ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga gwamnatin jihar, iyalansa da al’ummar Zamfara
- Shinkafi ya taɓa zama Kwamishinan Matasa da Wasanni kafin daga bisani a mayar da shi Ma’aikatar Kasuwanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana alhininsa kan rasuwar Kwamishinan Kasuwanci na jihar, Tasiu Musa Shinkafi.
Rahotanni sun bayyana cewa Tasiu Musa Shinkafi ya rasu ne ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamban 2026 a Kaduna, yana da shekara 50, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin gwamnan a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan
APC ta yi gyara a kwamitin kamfen din Tinubu bayan an yi abun kunya a idon duniya
Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba ga gwamnatin jihar da al’ummar Zamfara baki ɗaya
Abin da Gwamna Dauda Lawal ya ce
A cikin sanarwar, Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatin jihar ta samu labarin rasuwar kwamishinan cikin jimami, tare da miƙa wuya ga ƙaddarar Allah Maɗaukakin Sarki.
"Cikin baƙin ciki da miƙa wuya ga hukuncin Allah Maɗaukakin Sarki (T), muka samu labarin rasuwar Kwamishinan Kasuwanci, Tasiu Musa Shinkafi, wanda ya ba mu mamaki.
“Rasuwar Tasiu babban rashi ne, ba ga iyalansa da gwamnatin jihar kaɗai ba, har ma ga al’ummar Zamfara baki ɗaya.
“Za a riƙa tunawa da shi bisa jajircewarsa, gaskiyarsa da kuma ƙoƙarin da ya yi wajen yi wa Jihar Zamfara hidima.”
Tarihin hidimarsa a gwamnatin jihar
Gwamna Lawal ya bayyana cewa marigayin ya yi aiki tuƙuru a matsayin Kwamishinan Matasa da Wasanni kafin daga bisani a sauya masa wurin aiki zuwa Ma’aikatar Kasuwanci.
Ya ƙara da cewa Tasiu Shinkafi na daga cikin muhimman mambobin gwamnatinsa, kuma sun kasance abokan aiki da ’yan’uwa wajen gudanar da hidimar al’umma.
Gwamna Dauda ya ce gudummawar marigayin a harkokin mulki, siyasa da hidimar jama’a za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa.
A ƙarshe, Gwamna Dauda Lawal ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya kuma ba iyalansa ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.

Source: Original
Tsohon shugaban jami'ar OAU ya rasu
A wani labarin, kuma kun ji cewa rohon shugaban jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke jihar Osun, Farfesa Wale Omole, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, a gidansa, kamar yadda shugaban kungiyar Ijesa Society, Lateef Bakare, ya sanar a wata sanarwa da ya fitar.
Farfesa Wale Omole shi ne tsohon dalibi na farko a jami'ar Ife, wadda a yanzu ake kira Obafemi Awolowo University, da ya zama shugaban jami'ar. Ya rike mukamin daga shekarar 1991 zuwa 1999.
Asali: Legit.ng
