An Rasa Rayukan Mutane yayin Jana'iza, da Yawa Sun Raunata a Niger

An Rasa Rayukan Mutane yayin Jana'iza, da Yawa Sun Raunata a Niger

  • An kashe mutane biyu tare da jikkata wasu bayan barkewar rikicin ƙabilanci tsakanin wasu al’ummomi biyu a jihar Niger
  • Rikicin ya ɓarke ne yayin gudanar da jana’izar mamaci a yankin Warari da ke ƙaramar hukumar Rijau da ke jihar a Arewacin Najeriya
  • ’Yan sanda sun shiga tsakani tare da ’yan banga, inda suka shawo kan lamarin, yayin da bincike kan musabbabin rikicin ya fara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Niger - An kashe mutum biyu tare da jikkata wasu mutane bayan ɓarkewar rikicin ƙabilanci tsakanin mazauna ƙauyukan jihar Niger da ke fama da matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

Iran ta fitar da bidiyon rumbun makamai da ke karkashin kasa

An samu rikicikn ne a kauyukan Azayagun da Unguwan Dikko da ke yankin Sullubawa, gundumar Warari a ƙaramar hukumar Rijau ta jihar Niger.

An rayuka a Niger
Sufeta-janar na yan sanda, Rilwan Disu. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Rahotanni daga Zagazola Makama sun nuna cewa rikicin ya ɓarke ne yayin gudanar da jana’izar mamaci, inda mazauna ƙauyukan biyu da ke cikin al’ummar Kambari suka yi arangama kan wasu dalilai da ba a bayyana ba.

An bayyana sunayen mutanen da suka rasa rayukansu da Buni Galadima da Sambo Tsinkayi, waɗanda dukkaninsu maza ne kuma mazauna ƙauyen Azayagun.

’Yan sanda sun shiga tsakani

Majiyoyin ’yan sanda sun bayyana cewa an kai rahoton faruwar lamarin ga jami’in ’yan sanda na ƙaramar hukumar Rijau ta hannun jami’in da ke kula da ofishin ’yan sanda na Warari.

Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda tare da haɗin gwiwar ’yan banga sun garzaya zuwa ƙauyukan da abin ya shafa domin shawo kan rikicin.

Tawagar jami’an tsaron ta yi nasarar dawo da zaman lafiya a yankin, yayin da aka kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu da sauran waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Warari domin gudanar da binciken gawarwaki da ba su kulawar lafiya.

Kara karanta wannan

Hatsabibin ɗan bindiga da ya addabi jama'a ya sheƙa barzahu a Katsina

An fara binciken musabbabin rikicin

Rundunar ’yan sandan ta tabbatar da cewa an dawo da zaman lafiya a ƙauyukan biyu bayan shawo kan rikicin inda ta sha alwashin daukar matakan da suka dace.

Haka kuma, ta bayyana cewa an fara gudanar da bincike na farko domin gano ainihin abin da ya haddasa arangamar tsakanin al’ummomin da ke yankin.

Rahotanni sun kuma nuna cewa ƙauyukan biyu sun taɓa shiga irin wannan rikici a lokutan baya wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Yawan rikicin kabilanci a Najeriya na jawo koma baya ga al'ummomi da dama wanda ke faruwa a kusan dukan yankunan Najeriya baki daya.

An samu tashin hankali a Kaduna

Mun ba ku labarin cewa an shiga tashin hankali sakamakon rikici tsakanin wasu gungun matasa a unguwannin Kwaru da Unguwar Yero da ke jihar Kaduna.

An ce mutum uku sun samu raunuka a rikicin farko, yayin da ɗaya daga cikinsu ya rasu daga baya lamarin da ya tayar da hankula a yankin.

Yan sanda, DSS da jami’an MOPOL sun kai dauki yankuan da lamarin ya faru domin dawo da zaman lafiya inda aka ce mutane sun fara ci gaba da ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.