Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Ga Ta Kansa da Ya Yi Kokarin Tallata Tinubu a Taron Jama'a

Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Ga Ta Kansa da Ya Yi Kokarin Tallata Tinubu a Taron Jama'a

  • Jama’a sun yi ta rera sunan Peter Obi yayin da Benjamin Kalu ke kokarin neman goyon baya da tallata Shugaba Bola Tinubu a wani taro
  • Lamarin ya faru ne a yayin bikin al’adun Item Okpi da aka gudanar a Jihar Abia da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
  • Kalu, mataimakin shugaban Majalisar wakilai ya bukaci jama’a su zabi Tinubu, amma mutanen da ke wurin suka ci gaba da kiran sunan Obi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia, Nigeria - An samu wani yanayi mai daukar hankali a Jihar Abia, yayin da jama’a suka rika kidan sunan Peter Obi a lokacin da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ke kokarin yi wa Shugaba Bola Tinubu kamfe.

Hon. Kalu, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Bende, ya hau kan dandali domin neman goyon bayan Tinubu a yayin bikin Item Okpi.

Kara karanta wannan

"Abin da zai sa Tinubu ya samu gagarumar nasara a zaben shugaban kasa na 2027"

Benjamin Kalu.
Mataimakin Shugaban Majalisar wakilai, Rt. Hon. Benjamin Kalu Hoto: Benjamin Kalu
Source: Facebook

Premium Times ta ruwaito cewa bikin dai wani taro ne na shekara-shekara da al’ummar masarautar Item da ke Karamar Hukumar Bende a Jihar Abia ke gudanarwa domin raya al’adunsu.

Jama'a sun yi wa Benjamin Kalu turjiya

Wani faifan bidiyo da ya nuna Kalu yana kokarin shawo kan jama’a su mara wa yunkurin Tinubu na neman wa'adi na biyu a wurin taron, sai dai jama’ar sun nuna rashin amincewa da bukatarsa, inda suka rika kiran sunan Obi ba kakkautawa.

Obi, tsohon gwamnan Jihar Anambra, shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC a zaben 2027.

"Tinubu zai yi wa Abia abubuwa da dama. Ku zabi Tinubu a 2027. Shi ne mafi dacewa da Najeriya," in ji Kalu a wajen bikin.

Nan take jama’a suka fara rera sunan Obi.

Yadda aka rika kiran sunan Obi

Wata mata da ba a tantance ko wacece ba, wadda ke kan dandali, ta fara rera shahararriyar wakar yakin neman zaben Tinubu mai taken “On Your Mandate”.

Kara karanta wannan

Sarakunan Yarbawa a jihohin Arewa 19 sun dauki babban alkawari ga Tinubu

Sai dai jama’ar sun kara karfin muryoyinsu wajen kiran sunan Obi, ba tare da kula da kokarin mataimakin kakakin majalisar na dakatar da su ba.

"Da alama ba ku son jami’ar da Shugaba Tinubu ke shirin gina muku na," in ji Kalu da harshen Igbo, a lokacin da ya bayyana cewa abin ya fara bata masa rai.

Amma jama’ar sun yi biris da shi, inda suka kafa dagewa wajen kiran sunan Obi.

"Wadannan mutanen ba ’yan Item ba ne," in ji Kalu.

Yayin da Kalu ke magana, wata mata da ba a tantance ko wacece ba, ta fara rera wakar goyon bayan Obi. Sai dai ya umarce ta da ta rera wakar Tinubu, kuma ta yi hakan.

Duk da haka, jama’ar sun ci gaba da kiran sunan Obi, har ma lokacin da Kalu ya matsa zuwa gaban dandali domin sake neman goyon bayan jama’a ga yunkurin Tinubu na zarcewa kan karagar mulki.

"Obi, Obi!" jama’ar suka ci gaba da furtawa.

APC za ta fara kamfe a Abia

Kun ji cewa jam’iyyar APC a jihar Abia ta sanya ranar 16 ga Nuwamba, 2026, domin ƙaddamar da gangamin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya sanar da shirin rabon motoci sama da 100 ga mambobin APC masu biyayya ga jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262