Babbar Magana: Ana Shirin Amfani da Makami Mafi Hadari bayan Nukiliya a Yakin Amurka da Iran

Babbar Magana: Ana Shirin Amfani da Makami Mafi Hadari bayan Nukiliya a Yakin Amurka da Iran

  • Sojojin Amurka na tsara kai hare-hare kan cibiyoyin makamashi da na nukiliyar Iran, da amfani da bam mai hadari da ake kira “uwar bama-bamai”
  • Matakin zai iya ƙara tsananta yaƙin idan Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin komawa yaƙi kafin ko bayan zaɓen tsakiyar wa'adin mulki
  • Trump na fuskantar matsin lamba domin kawo ƙarshen yaƙin, yayin da ake ci gaba da nuna shakku kan ko hare-haren za su iya cimma manufofin Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Sojojin Amurka na tsara kai sababbin hare-hare kan kasar Musulunci ta Iran, ina aka ruwaito cewa suna duba yiwuwar amfani da bam ɗin da aka fi sani da “uwar dukkan bama-bamai."

Majiyoyi sun ce Amurka na shirin kai wadannan hare-hare ne kan cibiyoyin makamashi da wuraren nukiliyar Iran, idan Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin sake komawa yaƙi kafin ko bayan zaɓen tsakiyar wa'adin mulki.

Kara karanta wannan

Minista ya ɓallo ruwa a gaban ƙasashen duniya, ya yi maganar da ka iya juyo wa kan Tinubu

MUAB.
Makamin MUAB a wani sansanin sojin Amurka da ke Florida yayin da ake shirin gwaji a watan Maris, 2003 Hoto: DoD
Source: Getty Images

Wasu jami'an Amurka da dama da ke da masaniya kan lamarin ne suka tabbatar da hakan ga tashar CNN.

Amurka na shirin amfani da MUAB

Amfani da bam ɗin GBU-43/B Massive Ordnance Air Blast (MOAB), wanda shi ne bam mafi girma da ba na nukiliya ba a cikin makaman Amurka, a karon farko a yaƙin da ake yi da Iran, zai zama wani gagarumin ƙarin tsananta rikicin.

Sai dai majiyoyi da suka san shirin sojoji kan yiwuwar amfani da bam ɗin sun bayyana cewa akwai shakku kan ko hakan zai yi tasiri wajen cimma manufofin dabarun yaƙi da Trump ya bayyana ko kuma sauya yanayin yaƙin.

Trump na fuskantar matsin lamba na kawo ƙarshen yaƙin da jama'ar Amurka da dama ba sa goyon baya.

Hakan na faruwa ne yayin da 'yan jam'iyyar Republican ke shirin fuskantar yiwuwar fushin masu zaɓe a zaɓen tsakiyar wa'adin mulki mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ganduje, Shekarau da sauran jiga jigan APC da suka shiga kwamitin kamfen Abba

Ina aka kwana kan batun sulhu?

Babu wata alama mai ƙarfi da ke nuna cewa Amurka da Iran sun kusa cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen rikicin bayan fiye da watanni shida ana kai hare-haren bama-bamai.

Yayin da sojojin Amurka ke ci gaba da gabatar wa Trump da tsare-tsaren kai hare-hare kan sauran wuraren da suke ganin ya kamata a lalata a Iran, wasu jami'ai na ci gaba da nuna shakku a sirrance.

Shugaban Amurka ne kaɗai ke da ikon yanke irin wannan hukunci na kai hare-haren ko kuma akasin haka, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Donald Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House da ke birnin Washington DC Hoto: Aaron Schwartz
Source: UGC

Trump na neman kawo ƙarshen yaƙin

Tsawon watanni, Trump da masu ba shi shawara sun tattauna hanyoyin da za su iya zama tamkar “tabbataccen” ƙarshen yaƙin, musamman ta fuskar yadda za a sanar da jama'a sakamakon, saboda sun san Amurkawa ba su kaunar yakin.

Yayin da wasu jami'an gwamnatin Trump suka bayyana cewa a zahiri an riga an yi nasara a yaƙin, Trump ya yi taka-tsantsan a kalamansa na baya-bayan nan, inda ya ƙaurace wa ayyana nasara kai tsaye.

Kara karanta wannan

NCC ta ɓullo da wani tsari, mutane na iya asarar wayoyin da suka Ssaya da kuɗinsu a Najeriya

Iran ta gindaya sharudda 7 ga Amurka

Kun ji cewa Iran ta ce ba za ta sake bude mashigar Hormuz ba har sai an cika wasu sharudda bakwai da ta gindaya a yarjejeniyar wucin gadi da Amurka.

Kakakin Majalisar Iran, Mohammad Baqer Ghalibaf, ya ce Tehran ta yi watsi da matsin lambar Amurka, tana mai dagewa kan sharuɗɗanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262