Kotun Daukaka Kara Ta Canza Tunani kan Hana Musulmi Sanya Hijabi a Makarantar ISI

Kotun Daukaka Kara Ta Canza Tunani kan Hana Musulmi Sanya Hijabi a Makarantar ISI

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta umarci a dakatar da aiwatar da hukuncin hana sanya hijabi a makarantar ISI da ke jihar Oyo
  • Hakan ya biyo bayan korafin da kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya, MURIC ta shigar bayan hukuncin da kotun ta yanke a baya
  • MURIC ta bayyan shirinta na ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli bayan hukuncin da ya hana amfani da hijabi a makarantar ISI

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo, Nigeria - Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Ibadan ta umarci a dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke kwanakin baya, kan sanya hijabi a makarantar ISI da ke jami'ar Ibadan.

Kotun ta umarci dukkan ɓangarorin da ke shari'ar sanya hijabi da su tsaya a matakin da ake kafin ta yi hukuncin haramta sanya hijabin.

Kara karanta wannan

Bayan malamar Islamiyya, An kona gawar mutumin da kashe a Kano

Kotu.
Gudumar da alakali ke amfani da ita a kotu a Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Kotu ta hana tsangwamar ɗalibai

Kwamitin alkalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a K.I. Amadi ne ya bayar da umarnin yayin sauraron buƙatar ƙungiyar kare hakkin musulmi (MURIC), kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Kungiyar NURIC ta shigar da bukata gaban kotun daukaka kara, tana neman umarnin dakatar da aiwatar da hukunci har sai an kammala sauraron ƙarar.

Kotun ta kuma gargadi dukkan ɓangarorin da kada su ci gaba da tsangwama, razana ko ɗaukar wani mataki kan ɗalibai mata Musulmai da abin ya shafa har sai an yanke hukunci kan buƙatar da ke gabanta.

MURIC ta yi fatali da hana sanya hijabi

Takardun kotu sun nuna cewa an yi rajistar shari'ar da lamba CA/IB/347/2024, kuma tana cikin jerin ƙorafe-ƙorafen farar hula da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Ibadan ke saurare.

Lauyan kungiyar MURIC, Hassan Taiwo Fajimite, ya roƙi kotun da ta kare abin da ake taƙaddama a kai ta hanyar dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke ranar Juma'ar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Kotu ta shirya hukunci a shari'ar da hukumar EFCC ta nemi ƙwace kadarorin Malami

Ya ce Jami'ar Ibadan da makarantar ISI ba su da ikon hana ɗalibai mata Musulmai sanya hijabi ko ɗaukar matakin ladabtarwa a kansu muddin batun na gaban kotu.

Akintola.
Shigaban kungiyar kare hakkin musulmi ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola Hoto: @ImranMuhdz
Source: Twitter

Kotu ta dage zaman shari'ar hijabi

Alkalan sun kuma tambayi dalilin da ya sa aka fara ɗaukar mataki kan ɗaliban alhali har yanzu ba a fitar da kwafin hukuncin da aka tabbatar ba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu, kotun da ke zama a Ibadan ta umarci a ci gaba da yadda al'amura suke har zuwa ranar 7 ga Oktoba, lokacin da za a saurari buƙatar.

Yadda kotun ta haramta sanya hajabi a ISI

A wani rahoton, kun ji cewa kotun daukaka kara da ke zamanta a Ibadan ta haramtawa dalibai mata musulmi na Makarantar International School (ISI) sanya hijabi.

Kotun ta soke hukuncin Babbar Kotun Jihar Oyo, wacce ta amince dalibai mata su rika sanya hijabi a makarantar ISI tare da kayan makaranta.

Shari'ar ta samo asali ne bayan dalibai mata Musulmai 11 sun shigar da kara suna zargin mahukuntan makarantar da tauye musu 'yancinsu na sanya hijabi a matsayin wani bangare na kayan makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262