Kaico: Mutane da Dama Sun Mutu yayin da Suka Je Dibar Ganima Jikin Wata Tankar Fetur

Kaico: Mutane da Dama Sun Mutu yayin da Suka Je Dibar Ganima Jikin Wata Tankar Fetur

  • Ana fargabar mutane da dama sun mutu da wata tankar mai ta fashe a kan titin Benin-Lagos kusa da Oluku a birnin Benin na Jihar Edo
  • An ce mai ya kwarara daga tankar bayan ta faɗi, lamarin da ya jawo mutane suka yi tururuwa domin kwasar man fetur kafin ta kama da wuta
  • Kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a Edo ya nuna alhininta tare da kira da a tallafa wa waɗanda abin ya shafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo, Nigeria - An shiga fargaba a kan babban titin Benin-Lagos kusa da Oluku a birnin Benin na Jihar Edo, bayan fashewar wata tankar mai.

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin fashewar tanka da wutar da ta biyo baya ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da lalata dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Masoyan APC sun yi hatsarin mota a kan janyar zuwa gangamin Tinubu, Shettima

Jihar Edo.
Taswirar jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Leadership ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan tankar da ke ɗauke da man fetur ta faɗi, inda mai ya zube a ƙasa. Hakan ya jawo mutane suka yi tururuwa domin kwasar ganima.

Yadda tanka ta fashe a Edo

Wani ganau ya ce lamarin ya haifar da gobara da ta bazu a yankin, inda aka ruwaito cewa mutane da dama sun ƙone har ba a iya gane su.

An kuma ce shaguna da gine-gine da ke yankin sun lalace, yayin da mazauna unguwar da 'yan kasuwa suka ruga domin tsira da rayukansu.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu a hukumance ba.

An garzaya da waɗanda suka tsira da raunuka daban-daban zuwa Asibitin Koyarwa na Jami'ar Benin (UBTH), yayin da jami'an tsaro da jami'an kashe gobara suka haɗa kai wajen gudanar da ayyukan ceto.

Jam'iyyar APC ta nuna alhininta

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya rasu, an ɗauke gawarsa daga Abuja

Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC a Jihar Edo ya bayyana matuƙar alhininta, tare da miƙa ta'aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma yi wa waɗanda suka jikkata addu'ar samun sauƙi cikin gaggawa.

A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaranta, John Mayaki, ya fitar, kwamitin ya bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, tare da kira da a gaggauta tallafa wa waɗanda suka tsira da iyalan da fashewar tankar ta shafa.

Yan kwana kwana.
Jami'an hukumar kashe gobara suna kokarin shawo kan wutar da ta kama Hoto: Getty Images
Source: UGC

Mayaki ya ce:

“Muna tare da iyalan da wannan mummunan bala'i ya shafa. Muna alhini tare da su, kuma muna addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba su ƙarfin zuciyar jure wannan rashi.”

Ya kuma yaba wa babban daraktan kula da Asibitin Koyarwa na Jami'ar Benin, Farfesa Idia Nibokun Ize-Iyamu, bisa jagorantar ayyukan ba da agajin gaggawa a asibitin da kanta.

Mayaki ya kuma soki yunƙurin shigar da siyasa cikin wannan mummunan al'amari, wanda ya jawo asarar rayuka, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Motar gas ta kashe mutane a Kogi

Kun ji cewa wata motar gas ta fashe a wani wajen da sojoji suka kafa shinge a kan babbar hanyar Abuja-Lokoja a jihar Kogi.

Gobara ta kama motocin da suka dauko kaya guda uku kuma direbobi da mataimakan su sun kone, adadin wadanda suka rasa rai ya kai shida

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262