Badakalar Makamai: Buratai Ya Fadi Wadanda aka Tura wa Makudan Kudi
- Tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Yusuf Buratai mai ritaya, ya yi magana kan dala biliyan 1 da aka ware domin sayen makamai
- Buratai ya ce kudin bai bi ta hannunsa ko asusun sojojin kasa, ruwa da sama ba, yana mai cewa zarge-zargen karkatar da kudin sun samo asali ne daga siyasa
- Ya bukaci a samar da tsarin bayyana bayanan kwangilolin sayen makamai, tare da gudanar da bincike da gurfanar da jami’an tsaro idan suna da laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubucEditan Legit Hause-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Yusuf Buratai (Mai ritaya), ya bayyana cewa dala biliyan 1 da gwamnatin tarayya ta amince da warewa domin sayen makamai a lokacin da yake ofis.
Buratai ya ce Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ce ta amince da kudin, amma bai bi ta hannunsa ko asusun rundunonin sojin kasa, ruwa da sama ba.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan zarge-zargen da suka dabaibaye kudin, yana mai cewa zarge-zargen sun kasance na siyasa da kuma na mugunta.
Wadanda aka ba kudin makamai
Tsohon hafsan sojin ya ce ba shi da hannu wajen tafiyar da dala biliyan 1, domin Ma’aikatar Tsaro ce ta karbi kudin tare da kula da dukkan tsarin sayen makaman.
Ya ce rundunonin sojin kasa, ruwa da sama ba su samu ko dala guda daga cikin kudin domin gudanar da sayen makamai ba.
A cewarsa, zarge-zargen karkatar da kudin sun fara bayyana ne a lokacin yakin neman zaben shekarar 2019, lokacin da ’yan adawa suka yi ikirarin cewa an karkatar da kudin domin ayyukan zabe.
Buratai ya ce gwamnatin tarayya ta fito ta musanta zargin a lokacin, amma har yanzu abin ya ci gaba da bata sunan shugabannin rundunonin soji maimakon cibiyar da ta kula da kudin.
Ana so ma’aikatar tsaro ta yi bayani
Buratai ya soki Ma’aikatar Tsaro bisa rashin fito wa fili ta bayyana yadda aka raba kudin ko yadda aka bayar da kwangilolin sayen makaman.
Ya ce ya kamata a bayyana wa jama’a inda aka kashe kudin da kuma yadda aka gudanar da kwangilolin, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana.
Tsohon hafsan sojin ya ba da shawarar kafa wata kafar intanet ta musamman da za ta rika wallafa bayanai kan kwangilolin sayen makamai, kamfanonin da aka ba kwangilolin da kuma lokacin da ake sa ran kammala ayyukan.
Punch ta wallafa cewa ya ce za a iya wallafa wadannan bayanai bisa la’akari da bukatun tsaron kasa, ba tare da bayyana bayanan da za su iya jefa tsaron kasa cikin hadari ba.
Buratai ya jaddada cewa idan kafafen yada labarai suka tambayi inda kudin suka shiga, ya kamata amsar ta fito daga ma’aikatar da ta kashe kudin, ba daga jami’an soji da ba su taba rike su ba.

Source: Facebook
Sojoji kwance bama-bamai
A wani rahoton, kun ji cewa sojoji sun gano tare da lalata wasu bama-bamai da ’yan ta’adda suka dasa a hanyar Magami zuwa Hannutara da Dansadau, a karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Dakarun sun samu sahihan bayanai kan barazanar, inda suka tsare yankin tare da gudanar da bincike. Sun gano wurare biyu da aka dasa bama-baman.
Rundunar ta kara yawan sintiri da sa ido a yankin domin kare mazauna da hana sake aukuwar barazana. Ta kuma bukaci jama’a su kasance masu sanya ido.
Asali: Legit.ng


