Ahmad Tibi: Musulmi Ya Zama Mataimakin Shugaban Majalisar Isra'ila

Ahmad Tibi: Musulmi Ya Zama Mataimakin Shugaban Majalisar Isra'ila

  • An zaɓi ɗan siyasar Larabawa, Ahmad Tibi, a matsayin ɗaya daga cikin mataimakan shugaban majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset
  • Rahoto ya nuna cewa an amince da naɗin Tibi ne duk da adawar wasu ‘yan majalisar da ke goyon bayan haɗakar jam’iyyar gwamnati
  • Wannan naɗi na zuwa ne bayan zaɓen ‘yan majalisar dokokin Isra’ila da ya bai wa jam’iyyun Larabawa kujeru 19 cikin 120 na majalisar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Isra'ila – An zaɓi ɗan siyasar Larabawa, Ahmad Tibi, a matsayin mataimakin shugaban majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset, duk da adawar wasu ‘yan majalisar da ke cikin haɗakar jam’iyyar gwamnati.

Kwamitin Tsare-tsaren Majalisar ne ya amince da jerin sunayen mataimakan shugabanni tara na riƙon ƙwarya da ƙuri’u 13 kan 9, bayan muhawara mai zafi.

Kara karanta wannan

Yan takarar gwamnan ADC sun ɗauki zafi kan hukuncin hana Atiku takara a zaben 2027

Ahmad Tibi
Mataimakin shugaban majalisar Isra'ila, Ahmad Tibi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Al Jazeera ya nuna cewa ‘yan majalisar adawa sun goyi bayan jerin sunayen, yayin da mambobin haɗakar jam’iyyar gwamnati suka ƙi amincewa da shi.

An naɗa Tibi duk ya sha adawa

Kafin kaɗa ƙuri’ar, wasu ‘yan majalisar da ke goyon bayan gwamnatin sun nuna rashin amincewarsu da naɗin Ahmad Tibi.

Sai dai an gabatar da sunayen dukkan ‘yan takarar a matsayin jerin guda, maimakon kaɗa ƙuri’a kan kowane mutum daban-daban.

Hakan ya sa aka amince da sunayen wasu ‘yan majalisar da jam’iyyun haɗakar gwamnati ke adawa da su, ciki har da na Tibi.

Sauran sunayen da aka amince da su sun haɗa da Eitan Ginzburg, Yair Fink, Walid Taha, Limor Son Har-Melech, Michael Malkieli, Oded Forer, Yitzhak Pindrus da Boaz Bismuth.

Tarihin siyasar Ahmad Tibi

Tibi shi ne shugaban jam’iyyar Arab Movement for Change, wadda aka fi sani da Ta’al, kuma yana cikin haɗakar jam’iyyun Joint List.

Anadolu ta wallafa cewa ya fara zama ɗan majalisar Knesset ne a shekarar 1999, kuma a baya ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin shugaban majalisar.

Kara karanta wannan

ADC ta ce tabbas Atiku zai shiga takarar shugaban kasa na 2027

Naɗinsa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun da ke wakiltar Larabawan Isra’ila, wato Joint List da United Arab List (Ra’am), suka samu nasarar lashe kujeru 19 a zaɓen majalisar da aka gudanar a watan Oktoba.

Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sakamakon zaɓen ranar 27 ga Oktoba ya nuna cewa ƙungiyar Firaminista Benjamin Netanyahu ta samu kujeru 53 a majalisar mai kujeru 120.

Netanyahu ya yi sabani da Gadi

A wani labarin, kun ji cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na fuskantar saɓani da Gadi Eisenkot, wanda ake ganin zai iya maye gurbinsa a shugabancin gwamnati.

Eisenkot ya buƙaci Netanyahu da ya guji ɗaukar manyan matakan tsaro kafin kafa sabuwar gwamnati, yana mai gargaɗin cewa yin hakan na iya haifar da matsala.

Ya kuma nemi Antoni Janar na Isra’ila da ta tabbatar masa da samun bayanan sirri kan harkokin tsaro domin ya iya sa ido kan matakan da gwamnatin riƙon ƙwarya ke ɗauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng