Yadda aka Halaka Wani Mutum Saboda ya Goyi Bayan Batanci ga Annabi

Yadda aka Halaka Wani Mutum Saboda ya Goyi Bayan Batanci ga Annabi

  • Wani mutum 'dan kasar Hindu mai sana'ar tela a Indiya ya rasa ransa bisa zarginsa da goyon bayan batanci ga Annabi Muhammad SAW wanda wani yayi
  • Kanhaiya Lal ya dora wata wallafa a shafinsa yanar gizo inda ya marawa maganar wani kakakin jam'iyyar BJP da ya yi na batanci ga Annabi Muhammad, baya
  • Biyun da ake zargi da halakasa sun zo masa shagon dinkinsa ne a matsayin kwastomomi, daga bisani suka aikasa barzahu yayin da ya yi kokarin gwadasu kafin ya dinka musu kaya

Rajasthan, Indiya - Kanhaiya Lal, wani mutum 'dan kasar Hindu ya rasa ransa a Rajasthan da ke Indiya bisa zarginsa da goyon bayan wanda yayi batanci ga Annabi Muhammad.

A ranar Talata, wasu maza biyu da suka zo masa a matsayin kwastomomi sun kai farmaki gami da halaka Lai, wanda tela ne yayin da yake aunasu a shagonsa da ke anguwar Udaipur.

Kara karanta wannan

Gaskiya Tayi Halinta: Yadda Aka Tirsasa CJN Tanko Yayi Murabus Kan Dole

Rajasthan, Indiya
Yadda aka Halaka Wani Mutum Saboda ya Goyi Bayan Batanci ga Annabi. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

An yi bidiyon wanda lamarin ya auku dashi yayin da aka halaka shi tare da dorawa a yanar gizo.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, makasansa sun yi ikirarin cewa sun yi hakan ne don daukar fansa a kan mutumin bisa marawa maganar Nupur Sharma, wanda kakakin jam'iyyar Bharatiya Janata ta kasa ne (BJP), wacce ta janyo cece-kuce a kan Annabi Muhammad.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An gano yadda Sharma ya yi furucin, wanda ake gani a matsayin laifi kan Annabi Muhammad yayin wata muhawara a watan Mayu.

An zargi Lal da yin wata wallafa a shafin sada zumuntar zamani tare da marawa furucin Sharma.

Foreign Newspaper ta bayyana yadda aka gano biyun da ake zargi a bidiyon gami da kamasu.

Haka zalika, gwamnatin Indiya ta dakatar da amfani da yanar gizo na wani lokaci tare da haramta dandazon taro.

Kara karanta wannan

Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

Maganar da 'dan siyasan ya yi ta janyo zanga-zanga a wasu jihohin kasar, tare da janyo rikici da kasashen musulmai da dama wadanda suka hada da UAE, Iraq da Libya, inda suka yi Allah wadai da furucin Sharma.

Manyan 'yan siyasa sun yi Allah wadai da halaka mutumin a Indiya.

Haka zalika, wasu fitattun kungiyoyin musulunci sun nuna rashin jin dadinsu kan kisan.

"Daukar doka a hannun mutum gami da halaka mutum ta hanyar ayyanashi a matsayin mai laifi ba dabi'a mai kyau bace. Doka bata amince da haka ba kuma shari'ar musulunci bata amince ba," kamar yadda kungiyar shari'ar musuluncin Indiya ta bayyana a wata takarda.

A Najeriya, Deborah Samuel, wata daliba a Kwalejin ilimi na Shehu Shagari ta rasa ranta bisa furucin da tayi a watan Mayu wanda batanci ne ga Annabi Muhammad.

A farkon watan nan, Ahmad Usman, wani 'dan kungiyar 'yan sa kai mai shekaru 30 ya rasa ransa a Abuja bisa zarginsa da batanci ga fiyayyen halitta.

Kara karanta wannan

Manyan Sirruka Sun Sake Bayyana Kan Yaron Da Ekweremadu Ya Kai UK Don Cire Masa Koda

Bayan wasu kwanaki, an kone wata mata Hannah Saliu, wacce karuwa ce bayan an ga Kur'ani a dakinta a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel