An Zo Wajen: Tsohon Gwamna Ya Gano Dabarar Atiku kan Shirin Dawo da Tallafin Fetur

An Zo Wajen: Tsohon Gwamna Ya Gano Dabarar Atiku kan Shirin Dawo da Tallafin Fetur

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya kwatanta shawarar Atiku Abubakar kan tallafin man fetur da tikitin Musulmi da Musulmi na APC
  • Fayemi ya ce Atiku na amfani da batun tallafin man fetur ne a matsayin dabarar siyasa, ba wai wata manufar tattalin arziki ba
  • Tsohon ministan ya sake bayyana goyon bayansa ga cire tallafin man fetur, amma ya soki yadda gwamnatin Tinubu ta aiwatar da manufar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti kuma tsohon Ministan Ma’adinan Ƙasa, Kayode Fayemi, ya bayyana shawarar Atiku Abubakar kan tallafin man fetur a matsayin dabarar siyasa.

Fayemi ya ce matakin na Atiku ya yi kama da dabarar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi amfani da ita wajen gabatar da tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Kara karanta wannan

'Trump na goyon bayan shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur

Kayode Fayemi ya gano dabarar Atiku
Kayode Fayemi da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: Kayode Fayemi, Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise Tv a shirin Prime Time ranar Litinin, 7 ga watan Satumban 2026 yayin da ake ci gaba da muhawara kan tallafin man fetur.

“Dabarar siyasa ce”

Fayemi ya ce bai ɗauki shawarar Atiku ta dawo da tallafin man fetur a matsayin wata manufa ta tattalin arziki ba.

“Ra’ayina shi ne, shawarar Atiku kan tallafi a siyasance ta yi daidai da tikitin Musulmi da Musulmi da muka yi a 2023. Dabarar siyasa ce. Ba tsarin tattalin arziki ba ne,” in ji Fayemi.

Sai dai ya amince cewa wannan batu na iya samun karɓuwa daga ’yan Najeriya da cire tallafin man fetur ya shafa sosai.

Ya ce ’yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali sun fi damuwa da yadda za su samu sauƙin rayuwa fiye da muhawarar fasaha kan manufofin tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

An gano dan siyasar zai zama barazana ga sabon yunkurin hadakar 'yan adawa

Fayemi ya goyi bayan cire tallafi

Fayemi ya sake jaddada cewa yana goyon bayan cire tallafin man fetur, yana mai cewa ya daɗe yana fafutukar ganin an aiwatar da manufar.

Ya ce lokacin da yake shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF, ya shafe shekaru huɗu yana aiki kan batun cire tallafin.

“Na kasance kuma har yanzu ni mai goyon bayan cire tallafin man fetur ne. A matsayina na shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, na shafe shekaru huɗu ina wannan yaƙin,” in ji shi.

Ya kare Tinubu kan abin da ya gada

Fayemi ya ce Shugaba Bola Tinubu ya gaji wani aiki da gwamnatin da ta gabace shi ta riga ta kammala sosai kan batun cire tallafin man fetur.

Sai dai ya ce abin da bai gamsar da shi ba shi ne yadda aka aiwatar da manufar bayan Tinubu ya hau mulki.

“Abin da Shugaba Tinubu ya gada, cikin adalci, shi ne aikin da waccan gwamnatin ta riga ta kammala. Matsalar da nake da ita ita ce yadda aka aiwatar da shi,” in ji Fayemi.

Kara karanta wannan

"Na san komai," Tsohon gwamna ya 'tsoratar' da yan Najeriya kan shirin dawo da tallafin fetur

An tsara hanyar rage wa talakawa raɗaɗi

Tsohon gwamnan ya ce tun kafin cire tallafin, gwamnonin jihohi sun haɗa kai da gwamnatin tarayya da Bankin Duniya domin tsara hanyar rage wa ’yan Najeriya mafiya rauni wahalar da manufar za ta haifar.

Ya ce an kafa wani kwamiti da ya yi aiki kan samar da tsarin tallafin jinƙai domin kare ɓangaren al’umma da ke cikin mafi tsananin buƙata.

Fayemi ya ce wannan shiri an tsara shi ne domin rage tasirin cire tallafin man fetur ga masu ƙaramin ƙarfi da kuma sauran ’yan Najeriya da za su fi fuskantar matsalar tattalin arziki

Kayode Fayemi ya yi magana kan Atiku
Kayode Fayemi na jawabi a wajen taro Hoto: Kayode Fayemi
Source: Facebook

Trump na goyon bayan Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Shugaban Amurka Donald Trump na goyon bayan shirinsa na dawo da tallafin man fetur.

Atiku ya sha alwashin dawo da tallafin man fetur, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage nauyin tsadar rayuwa da ke addabar ‘yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng