Rigima Sabuwa: Jiragen Yaki Sun Yi Barin Wuta a Saudiyya, an Tafka Asara
- Kakakin mayakin Houthi, Yahya Saree, ya ce hare-haren da suka kai Saudiyya sun kasance daidai kuma kai tsaye, inda suka yi barna sosai a cibiyoyin makamashin ƙasar
- Ya zargi Saudiyya da kai hare-hare 121 kan wasu yankunan Yemen, lamarin da ya ce ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, ciki har da mata da yara
- Houthi sun ce za su mayar da martani mai ƙarfi idan Saudiyya ta ci gaba da kai musu hare-hare, yayin da Kuwait ta yi Allah wadai da harin da aka kai Riyadh
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Sana’a – Kakakin sojojin Houthi na Yemen, Yahya Saree, ya ce ƙungiyar ta kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa kan wasu muhimman wurare a Saudiyya.
Saree ya bayyana cewa hare-haren da aka kai sun yi sanadiyyar lalacewa mai yawa a wasu cibiyoyin makamashi na Saudiyya.

Source: Getty Images
An kai hari kan cibiyoyin Aramco
Rahoton Al Jazeera ya nuna cewa Yahya Saree ya ce Houthi sun kai hari kan cibiyoyin kamfanin Aramco da ke Abha, Najran da Jizan.
A bayanan da ya yi, ya ƙara da cewa an kuma kai hari kan sansanin sojoji na Khamis Mushait.
A cewarsa, an gudanar da hare-haren ne ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu linzami da dama da kuma jirage marasa matuƙa.
Houthi ta zargi Saudi
Rahotanni sun nuna cewa Saree ya zargi Saudiyya da ƙaddamar da abin da ya kira mummunan hari da rashin adalci kan al'ummar Yemen.
Ya ce Saudiyya ta kai hare-hare 121 ta sama kan yankunan Marib, al-Bayda, Hodeidah, Taiz da al-Jawf.
Iran International ta wallafa cewa ya ce hare-haren sun kashe mutane da dama, ciki har da mata da yara.

Source: Getty Images
Saree ya ce Saudiyya ce ke da alhakin ƙara tsananta rikicin, yana mai gargadin cewa duk wani sabon hari kan Yemen zai fuskanci martani mai tsauri.
Ya ce:
“Ba za mu yi shakkar ƙaddamar da hare-hare masu ƙarfi da faɗi fiye da waɗanda muka kai ba.”
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Kuwait ta bayyana hare-haren a matsayin take haƙƙin ƙasar Saudiyya da kuma barazana kai tsaye ga tsaro da lafiyar al'ummarta.
Iran ta gargadi Koriya ta Kudu
A wani labarin, mun ruwaito cewa ma'aikatar harkokin wajen Iran ta gargadi Koriya ta Kudu kan tura sojoji ko shiga ayyukan Amurka a Mashigar Hormuz, tana mai cewa hakan zai hifar da “mummunan sakamako”.
A ranar Juma'a, Seoul ta ce tana nazarin yiwuwar bayar da gudunmawa ga ƙoƙarin tsaron Amurka a Mashigar Hormuz, wadda Iran ta fi samun iko da ita tun bayan barkewar yaƙi da Amurka a ranar 28 ga Fabrairu.
Iran ta gargadi Koriya ta Kudu kan abin da ya kira matsin lamba da tsoratarwa daga Amurka, yana mai cewa tura soji Tekun Farisa ko Mashigar Hormuz zai zama goyon bayan wanda ya fara kai hare-haren.
Asali: Legit.ng

