Abin Al’ajabi: Mutum Mutumi Sun Yi Zanga Zanga, Suna Neman Guraben Ayyuka

Abin Al’ajabi: Mutum Mutumi Sun Yi Zanga Zanga, Suna Neman Guraben Ayyuka

  • Mutum-mutumi sun gudanar da zanga-zanga a Warsaw, Poland, suna neman a tsaurara dokokin AI da kare ayyukan yi daga barazanar fasaha
  • Masu zanga-zangar sun ce mutum-mutumi da tsarin AI na iya maye gurbin ma’aikata, don haka ake bukatar dokoki da za su kare ma’aikata
  • Ministar Harkokin Dijital ta Poland ta yi gargadin cewa mutum-mutumin da AI ke sarrafawa na iya zama babbar barazana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Warsaw, Poland - A ranar Litinin, an yi zanga-zanga ta musamman a birnin Warsaw da ya mutanen duniya mamaki.

Kimanin mutum-mutumi 30 suka fito titunan Warsaw domin nuna adawa da kuma yin zanga-zanga da barazanar AI.

Mutum-mutumi 30 sun yi zanga-zanga a Poland
Mutum-mutumi 30 lokacin da suke zanga-zanga a birnin Warsaw na Poland. Hoto: AFP.
Source: UGC

Zanga-zangar mutum-mutumi ta ja hankali

Zanga-zangar ta mayar da hankali kan yadda basirar wucin gadi da sarrafa ayyuka ta atomatik ke kara barazana ga guraben ayyukan yi ga mutane, cewar Euro News.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta barke a Sokoto kan tsare malamin addinin musulunci

Mutum-mutumin sun taru a wajen Ma’aikatar Harkokin Dijital ta Poland, dauke da tutoci, suna zagayawa tare da gabatar da sakonni kan bukatar tsaurara dokokin AI.

Sun kuma yi kira da a kara kare ma’aikatan da ayyukansu ka iya shiga hadari sakamakon bullar sabbin fasahohi masu tasowa cikin sauri a duniya.

An shirya zanga-zangar ne ta Democratism, wata kungiya da ke mayar da hankali wajen karfafa tattaunawar jama’a kan tasirin basirar wucin gadi da mutum-mutumi.

Daya daga cikin mutum-mutumin da suka halarci zanga-zangar shi ne Agibot A3, wani mutum-mutumi mai kama da dan Adam wanda AI ke sarrafawa.

Agibot A3 ya shaida cewa manufar zanga-zangar ita ce nuna cewa fasahar mutum-mutumi ta zamani ba mafarki ko abu mai nisa ba ce.

“Mutum-mutumin da ke nan suna nuna cewa wannan fasaha ta riga ta zama gaskiya."

Kara karanta wannan

Iran ta fuskanci Koriya ta Kudu, ta mata gargadi kan hada kai da Amurka

In ji Agibot A3.

Mutum-mutumi 30 sun yi zanga-zanga a Poland
Shugaban kasar Poland, Karol Nawrocki yayin bikin tunawa da mazan jiya a Warsaw. Hoto: Artur Widak/NurPhoto.
Source: Getty Images

Yadda suka tura sakonni ga hukumomi

Jerin masu zanga-zangar ya kunshi nau’o’in mutum-mutumi daban-daban, ciki har da wadanda suke iya tafiya da kafafu biyu da kuma masu kafafu hudu kamar karnuka.

Ta hanyar lasifika, masu zanga-zangar sun gabatar da sakonni kamar “Ku kare guraben ayyukan yi”, “Lokaci ya yi da dokoki” da kuma “Kada ku jira, ku tsara dokoki”.

Grzegorz Kulis, daya daga cikin masu shirya zanga-zangar, ya ce manufarsu ita ce jawo hankalin jama’a kan yiwuwar mutum-mutumi da AI su maye gurbin mutane.

Kulis ya ce:

“Musamman muna son magance batun yiwuwar mutum-mutumi masu kama da mutane da kuma basirar wucin gadi su maye gurbin mutane a ayyukan tunani.
“Idan ba mu dauki mataki yanzu ba, nan ba da jimawa ba za mu fuskanci matsala."

Kulis ya ce sanya mutum-mutumi a tsakiyar zanga-zangar an yi hakan ne da gangan, domin nuna yadda fasahar mutum-mutumi ke samun ci gaba cikin sauri.

Kara karanta wannan

Jamhuriyar Nijar ta faɗi ƙasashen da take zargi da yunkurin yi mata juyin mulki

Ya ce ikon da mutum-mutumin ke da shi na gudanar da ayyuka da kansa a wuraren jama’a ya nuna irin saurin da fasahar mutum-mutumi ke samu, cewar Channels TV.

Yadda mutum-mutumi mace ke ba raba abinci

An ji cewa an gano wata mutum-mutumi wacce ke aikin bada abinciki a gidan cin abinci tana aikinta a yanayin da ya sa mutane dariya.

A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, mutum-mutumin ka kawo kwanon abinci sannan ta daura shi a kan tebur.

Tana ta abun sai kace wani na amfani da na'urar rimot wajen bata umurni kan abun da za ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.